"Akwai Matsala," Hakeem Baba Ahmed Ya Ƙara Fallasa Abin da Ya Gani a Gwamnatin Tinubu

"Akwai Matsala," Hakeem Baba Ahmed Ya Ƙara Fallasa Abin da Ya Gani a Gwamnatin Tinubu

  • Hakeem Baba-Ahmed ya ce ya karɓi muƙami a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ne domin ba da gudummuwa wajen gyara barnar Muhammadu Buhari
  • Sai dai tsohon hadimin mataimakin shugaban ƙasar ya ce sai da ya karɓi muƙamin sannan ya gane cewa babu wani shiri da ake yi na gyara
  • Dr. Hakeem Baba-Ahmed ya ƙara da cewa bai yi nadamar karɓar muƙamin ba amma kuma ba zai ƙara aiki a gwamnatin Shugaba Tinubu ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon mai ba mataimakin shugaban ƙasa shawara kan harkokin siyasa, Hakeem Baba-Ahmed ya ce ya karɓi muƙamin da Bola Tinubu ya ba shi ne domin a gyara ƙasa.

Hakeem ya bayyana cewa ko kaɗan bai yi nadamar karɓar muƙami a gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ba.

Hakeem Baba Ahmed da Tinubu.
Hakeem Baba Ahmed ya ce bai ga alamar gwamnatin Tinubu zs ta gyara ƙasar nan ba Hoto: @OfficialABAT
Source: Twitter

Hakeen Baba-Ahmed wanda ya yi aiki a ofishin mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya faɗi haka ne a wata hira da Channels tv.

Kara karanta wannan

"Ɗan Arewa kaɗai," Dele Momodu ya faɗi wanda zai iya kayar da Shugaba Tinubu a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin Hakeem Baba-Ahmed na aiki da Tinubu

Ya ce aiki a gwamnatin Tinubu, wacce ta gaji komai a lalace daga hannun Muhammadu Buhari, shi ne mafi girman sadaukarwar da kowame ɗan ƙasa zai iya yi.

"Aiki a gwamnatin Tinubu da ta gada ƙasar da Buhari ya lalata, shi ne mafi girman aikin kishin ƙasa da kowane ɗan Najeriya mai kishi zai iya yi.
"Ba za ka iya juya baya ga wata gwamnati da ta ce zo ka taimaka wajen gyara ƙasa ba, bayan an lalata ta.
"Na yi murabus ne kawai saboda ban ga alamar himma da ke nuna da gaske gyara ƙasar ake son a yi ba. Maimakon gyara, sai ƙasar ta kara tabarbarewa."

- Hakeem Baba-Ahmed.

Hakeem zai ƙara karbar aiki a gwamnatin Tinubu?

Sai dai, da aka tambaye shi ko zai karɓi irin wannan damar a karo na biyu, ya amsa da cewa, “A bisa yadda gwamnatin Tinubu ke tafiya yanzu, A’a.”

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Okowa ya bayyana lokacin da Atiku zai fice daga jam'iyyar PDP

Tsohon hadimin shugaban ƙasa ya ce ba zai iya ci gaba da aiki da gwamnati da a ganinsa ta riga ta sauka daga amanar da al'umma suka ba ta na kawo sauyi ba.

Dr. Hakeem Baba Ahmed.
Hakeem Baba Ahmed ya ce ba zai kuma karɓar aiki a gwamnatin Tinubu ba Hoto: Dr. Hakeem Baba-Ahmed
Source: Twitter

Hakeem Baba Ahmed ya ce gwamnatin Tinubu ta kaucewa alƙiblar gyara ƙasa musamman wajen yaki da talauci da rashin tsaro a Arewa, wanda ya ce sun kara muni a ƙarƙashin Tinubu.

Ya ce ko da shugaban ƙasa ya nemi ya gana da shi a sirrance, ya ƙi amincewa, domin da ya je, zai faɗa masa abubuwan da watakila ba zai so jinsu ba, ciki har da shawarar kada ya nemi tazarce a 2027.

Me yasa Hakeem Baba Ahmed ya yi murabus?

A wani labarin, kun ji cewa Hakeem Baba Ahmed ya bayyana dalilinsa na ajiye muƙamin mai ba mataimakin shugaban ƙasa shawara kan harkokin siyasa.

Hakeem ya ce shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ba shi da lokacin da zai zauna ya tattauna da hadimansa kan batutuwan da suka shafi jama'a.

Ya ce tun da ya karɓi mukamin bai taɓa samun damar zama da Tinubu ba, shi yasa ya yanke shawarar yin murabus.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262