Gwamnan Gombe da Sauran Jihohin APC da Suka Karyata Cewa za Su bi Atiku PDP

Gwamnan Gombe da Sauran Jihohin APC da Suka Karyata Cewa za Su bi Atiku PDP

A makon da ya wuce aka fara rade radin cewa wasu gwamnonin jami'iyyar APC za su iya juya baya ga shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027.

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Yayin da shugabannin APC ke ikirarin cewa manyan PDP na shirin sauya sheka, an yi rade radin cewa wasu gwamnonin APC za su juya wa Bola Tinubu baya.

Jim kadan bayan fitar jita jitar, gwamnonin APC da aka zarga suka fara martani suna nesanta kansu daga maganar.

Gwamnoni
Gwamnonin APC sun karyata maganar komawa PDP. Hoto: Nasir Idris|Mamman Mohammed|Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

A wannan rahoton, mun tattaro muku gwamnonin da aka zarga da irin martanin da suka yi kan lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnonin APC da ake zargin za su koma PDP

Wani shahararren mai amfani da kafar sada zumunta ta Facebook, George Udom ya wallafa a shafinsa cewa gwamnonin APC biyar za su hade da Atiku Abubakar kafin 2027.

Kara karanta wannan

Ganduje ya fadi yadda guguwar Tinubu ke shirin gamawa da PDP a Najeriya

Tinubu
Bola Tinubu da Kashim Shettima. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Gwamnonin da ya lissafa sune:

1. Inuwa Yahaya (Gombe)

2. Mai Mala Buni (Yobe)

3. Nasiru Idris (Kebbi)

4. Hyacinth Alia (Benue)

5. Umaru Bago (Niger)

Baya ga haka, ya yi ikirarin cewa Farfesa Babagana Umara Zulum na jihar Borno zai koma wata jam'iyya idan Bola Tinubu bai tafi da Kashim Shettima ba a 2027.

Martanin da gwamononin APC suka yi

1. Gwamnan Gombe ya ce yana tare da APC

Mai magana da yawun gwamnan jihar Gombe, Ismaila Uba Misilli, ya karyata jita jitar cewa Alhaji Inuwa Yahaya zai koma PDP.

Inuwa
Gwamnan Gombe ya ce yana nan a APC daram. Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Twitter

Ismaila Misilli ya wallafa a Facebook cewa:

“Wannan ƙaryar da ake yaɗawa abin dariya ce kuma ta nuna irin halin da masu yaɗa ta ke ciki.
"Waɗanda suka rasa amincewar jama’a yanzu sun koma hada tatsuniya don kawai su ji an ambace su.”

Ya ƙara da cewa babu wani abu da zai girgiza haɗin kan shugabannin jam’iyyar APC a jihar Gombe.

Kara karanta wannan

El-Rufa'i ya gano wanda ya fi dacewa ya mulki Najeriya a 2027

2. Gwamnan Yobe ya musanya batun sauya sheka

Mai magana da yawun gwamnan Yobe, Mamman Mohammed ya karyata ikirarin da George Udom ya yi a wani sako da ya wallafa a Facebook.

MAi Mala
Mai Mala Buni ya karyata jita jitar fita a APC. Hoto: Mamman Mohammed
Source: Facebook

Mamman Mohammed ya bayyana cewa:

“George Udom ya nuna jahilcinsa da rashin hangen nesa, kuma ya nuna cewa yana ƙoƙarin yi wa Atiku Abubakar hidima ta hanyar ƙirƙirar labaran ƙarya da ba su da tushe.”
“Ya kamata George ya sani cewa Gwamna Buni ba dan jam’iyya ne kawai ba.
"Shi jigo ne a APC, wanda ya yi shekara biyu a matsayin Sakataren jam’iyya na kasa da kuma Shugaban rikon kwarya.

3. Gwamnan Kebbi yana nan daram a APC

Gwamna Idris mai rike da sarautar Kauran Gwandu, ya jaddada cewa ya himmatu wajen cika alkawurran APC ga al’ummar Kebbi da tallafa wa manufofin gwamnatin Bola Tinubu.

Gwamnan Kebbi
Gwamnan Kebbi ya ce ba zai bar APC ba. Hoto: Kebbi State Government
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta rahoto gwamnan Kebbi ya ce:

"Idan wani ya sake faɗa muku Kauran Gwandu zai bar APC, ku fada masa cewa Kaura ne mutum daya tilo da zai tsaya a APC komai wuya."

Kara karanta wannan

Tsofaffin shugabanni 5 a zamanin Buhari da EFCC ke bincike a gwamnatin Tinubu

Sanarwar da jami’in yaɗa labaransa, Ahmed Idris, ya fitar, ta nanata cewa Kebbi na nan daram cikin APC, kuma jita-jitar da ake yadawa aikin ‘yan siyasa ne kawai.

El-Rufa'i ya ce za su kifar da Tinubu a 2027

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya yi magana kan komawar gwamnonin PDP jam'iyyar APC.

Tsohon gwamnan ya ce basu dogara da gwamnoni ba wajen ci zaben 2027, za su mayar da hankali ne kan masu kada kuri'a.

Ya kara da cewa ko a zaben 2023, jihohin APC da ke da gwamnoni kamar Kaduna, Legas da Gombe sun sha kaye a hannun PDP a zaben shugaban kasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng