Bayan Komawa APC, Okowa Ya Fadi Nadamarsa kan Takara da Atiku a 2023

Bayan Komawa APC, Okowa Ya Fadi Nadamarsa kan Takara da Atiku a 2023

  • Tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya yi magana kan takarar da ya yi a zaɓen shugaban ƙasa na 2023
  • Ifeanyi Okowa ya bayyana cewa ya yi nadamar amincewa ya zama mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar
  • Okowa wanda ya koma APC ya nuna cewa takarar da ya yi ta saɓa da muradin al'ummar jiharsa a lokacin zaben

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Delta - Tsohon gwamnan Jihar Delta, Dr. Ifeanyi Okowa, ya bayyana nadamarsa kan amincewar da ya yi ya zama mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, a zaɓen 2023.

Ifeanyi Okowa ya bayyana cewa amincewar da ya yi don zama abokin takarar Atiku, ya saɓawa muradin mutanensa.

Okowa da Atiku
Okowa ya ce ya yi nadamar yin takara da Atiku Hoto: Dr. Ifeanyi Okowa
Source: Twitter

Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin 'Morning Show' na tashar Arise Tv a ranar Talata.

Kara karanta wannan

2027: Tsohon na kusa da Peter Obi ya fadi abin da Tinubu zai yi idan babu hadaka

Meyasa Okowa ya yi nadamar takara da Atiku?

Okowa ya bayyana cewa amincewar da ya yi ta karɓar matsayin ba ta yi daidai da ra’ayin mafi yawan al’ummar jihar Delta ba.

Ya kare aikin da ya yi a gwamna, musamman a ɓangaren samar da ababen more rayuwa, kula da lafiyar mata da yara kyauta, da kuma nasarorin da gwamna mai ci Sheriff Oborevwori ke samu.

Amma ya amince cewa yarda ya shiga tikitin Atiku a 2023 ya jawo masa babbar asara a siyasa.

“Ko a lokacin da muke yaƙin neman zaɓe, na lura cewa mutanenmu ba su so wani ɗan Arewa ya sake zama shugaban ƙasa.
"Amma tuni jam’iyyar ta yanke shawara a matakin ƙasa, kuma ni aka zaɓa. Duk da haka, idan na yi duba a baya, na amince cewa ya kamata na saurari muradin mutanena."

- Ifeanyi Okowa

Okowa ya magantu kan rashin nasarar PDP a Delta

Kara karanta wannan

Shirin Bola Tinubu da Wike kan Gwamna Fubara da aka dakatar

Ya danganta rashin nasarar PDP a zaɓen shugaban ƙasa a Delta da rashin bin ra'ayin da al’umma suke so.

Okowa ya bayyana cewa ko da yake ya tsaya ne saboda biyayya ga jam’iyya, yankin Kudu ne ke da muradin samar da wanda zai gaji Shugaba Muhammadu Buhari.

Ifeanyi Okowa
Ifeanyi Okowa ya tabo batutuwan siyasa Hoto: Dr. Ifeanyi Okowa
Source: Facebook

Sai dai, Okowa ya nuna cewa abubuwa sun sauya ne jim kaɗan bayan haka, yayin da PDP ta samu nasara a zaɓen gwamna inda ta lashe ƙananan hukumomi 21 daga cikin 25 a jihar.

“Hakan ya nuna cewa mutanenmu har yanzu suna da ƙwarin gwiwa a kai na da jam’iyyarmu. Suka ce ‘ka yi mana aiki, kuma zamu goyi bayan wanda ka zaɓa a matsayin magajinka’. Kuma sun yi hakan."

- Ifeanyi Okowa

An ba Atiku shawara kan zaɓen 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ɗan majalisar wakilai, Tajudeen Yusuf, ya ba Atiku Abubakar shawara kan babban zaɓen 2027.

Tajudeen Yusuf ya buƙaci Atiku Abubakar ya haƙura da sake neman zama shugaban ƙasan Najeriya.

Tsohon ɗan majalisar ya bayyana cewa kamata ya yi Atiku ya haƙura domin ba da dama ga ɗan Kudu ya zama ɗan takarar PDP a 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng