"Tinubu Ya Gaza": Jigo a APC Ya Fara Hango Makomar Kujerar Shugaban Kasa

"Tinubu Ya Gaza": Jigo a APC Ya Fara Hango Makomar Kujerar Shugaban Kasa

  • Ƴaƴan jam'iyyar APC mai rike da mulki sun fara magana kan kamun ludayin gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu
  • Wani jigo a jam'iyyar APC, Jesutega Onokpass ya bayyana cewa shugaban ƙasan ya gaza wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansa
  • Onokpass ya bayyana cewa sauya sheƙar da ƴan adawa suke yi zuwa APC ba zai taimake ta ba a babban zaɓen shekarar 2027

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Wani jigo a jam'iyyar APC, Jesutega Onokpasa, ya yi magana kan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Jesutega Onokpasa ya ce Shugaba Bola Tinubu ya gaza matuƙa dangane da yadda gwamnatinsa ke tafiya.

Mai girma Bola Tinubu
Jesutega Onokpasa ya ce Tinubu ya gaza Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Jigon na jam'iyyar APC ya bayyyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Arise Tv.

Me jigon APC ya ce kan Bola Tinubu?

Kara karanta wannan

2027: Tsohon shugaban PDP ya fadi babbar matsala 1 da Tinubu, APC za su fuskanta

Jesutega Onokpasa ya yi gargaɗin cewa Tinubu na iya zama shugaban ƙasa na wa’adi ɗaya idan bai gyara ayyukansa ba.

Haka kuma, Onokpasa ya nuna mamaki kan yadda gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori, wanda ya kira ɗan uwansa, ya sauya sheka zuwa APC.

Jigon ya ce sauya sheƙar gwamnan zuwa jam’iyya mai mulki ba zai ƙara wata kima ko amfani ga jam’iyyar ko jihar Delta ba.

Onokpasa ya ƙara da cewa kamata ya yi APC ta mai da hankali kan yin shugabanci mai kyau, maimakon mayar da hankali wajen karɓar ƴan adawa.

'Dan APC ya magantu kan sauya sheƙa

Ya ce sauya shekar ƴan adawa zuwa APC yana tauye tsarin dimokuradiyya.

"Ba wai kawai batun mutane na sauya sheka zuwa jam’iyyarmu ba ne. Tambaya ita ce, muna yin mulki da kyau kuwa? A wannan ɓangare, mun gaza matuƙa."
"Shugaba Bola Tinubu ya ƙasa matuƙa wajen yin mulki da kyau, samar da abinci ga ƴan Najeriya, da kuma kawo sauki a cikin wannan mawuyacin lokaci."
"Gwamna Sheriff Oborevwori, wanda kwanan nan ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyarmu, ɗan uwana ne. Ban san dalilin sauya shekar sa zuwa jam’iyyarmu ba. Bai sanar da ni ba. Ina yi masa fatan alheri."

Kara karanta wannan

Da gaske gwamnonin APC 5 za su koma tafiyar Atiku? Gwamna Buni ya yi magana

"Ban ga wani amfani da hakan zai kawo masa ba, ko ga jam’iyyarmu, ko ga jihar Delta ba."

- Jesutega Onokpasa

Bola Tinubu
Jigo a APC ya ce Tinubu ya kasa sauke nauyin da ke kansa Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook
"Tara mutane cikin jam’iyya guda ba dimokuradiyya ba ce. Abin da ya kamata shi ne a riƙa samun adawa, domin mutane su rika bayyana ra’ayinsu. Yin jam’iyya ɗaya a ƙasa abu ne da ba zai yiwu ba."
"Zan faɗa muku kyauta cewa, idan muka ci gaba da tafiya haka, duk waɗannan sauya sheƙar ba za su taimake mu ba a 2027."
"Idan ba mu yi hankali ba, Bola Tinubu zai zama shugaban ƙasa na wa’adi guda. Ku rubuta wannan ku ajiye."

- Jesutega Onokpasa

Masanin siyasa ya ba El-Rufai shawara kan Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani masani kan al'amuran siyasa, Majeed Dahiru, ya ba Nasir El-Rufai kan Shugaba Bola Tinubu.

Majeed Dahiru ya bayyana cewa tsohon gwamnan na jihar Kaduna zai iya kawo ƙarshen mulkin Tinubu a 2027.

Ya nuna cewa hakan zai yiwu ne idan El-Rufai ya sanya masu ruwa da tsaki a Arewa suka goyawa Peter Obi baya a zaɓen.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng