Majalisa Ta Hargitse ana Shirin Tattauna Maganar Dakatar da Gwamna Fubara

Majalisa Ta Hargitse ana Shirin Tattauna Maganar Dakatar da Gwamna Fubara

  • Rahotanni na nuni da cewa 'yan majalisar wakilai sun kaure da cacar baki ana shirin fara tattauna dokar ta-baci a jihar Rivers
  • Hakan na zuwa ne bayan Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci tare da dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa
  • Duk da amincewa da matakin da Bola Tinubu ya yi, shugaban kasar zai jira yardar majalisar tarayya kafin tabbatar da hukuncin a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - ‘Yan majalisar wakilai sun yi cacar baki yayin da za a fara muhawara kan dokar ta-baci da Bola Ahmed Tinubu ya ayyana a Jihar Rivers.

Tun kafin zaman majalisar ya kankama, ‘yan majalisar sun rika musayar yawu kan matakin da shugaban kasa ya dauka.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya sa labule da 'shugaban riko' na jihar Ribas, bayanai sun fito

Majalisa
An samu hargitsi a majalisar wakilai kan sanya dokar ta baci a Rivers. Hoto: Abbas Tajudeen
Asali: Facebook

A wani bidiyo da gidan talabijin na AIT ya wallafa a X, an hango wasu 'yan majalisar wakilai mata suna kokarin ba hammata iska a zauren majalisar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shirin majalisa kan dokar ta-tacin Rivers

A ranar Talata shugaban kasa ya dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, Ngozi Odu, da kuma 'yan majalisar dokokin jihar.

Bayan haka, ya nada tsohon mataimakin hafsan sojan ruwa, Ibok-Ete Ibas, a matsayin mai rikon kwarya domin tafiyar da jihar har sai an samu mafita.

Kakakin majalisar wakilai, Akin Rotimi, ya bayyana cewa Shugaban kasa ya tuntubi majalisar tarayya kafin daukar matakin.

Gwamna Fubara
Gwamnan jihar Rivers da aka dakatar. Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Rotimi ya ce Tinubu ya gana da manyan shugabannin majalisar, ciki har da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas.

Sauran da suka halarci ganawar sun hada da Mataimakin Kakakin Majalisar, Benjamin Kalu, da shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Michael Bamidele, da Julius Ihonvbere.

Kara karanta wannan

Rivers: Ƴan majalisa sun fadi matsayarsu kan dokar ta ɓaci, sun fadi mai laifi

Takaddama a zauren majalisar wakilan tarayya

A yayin zaman majalisar na yau, wasu ‘yan majalisa sun fara ihu suna cacar baki, alamar da ke nuna za a iya samun sabani kan matakin da za su dauka a kan dokar ta-baci a Rivers.

Rahoton The Cable ya nuna cewa akwai alamu wasu ‘yan majalisa sun nuna rashin amincewa da matakin, suna zargin cewa matakin na da nasaba da siyasa, ba wai domin kare doka da oda ba.

Kakakin majalisar, Akin Rotimi ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya riga ya aika da wasikar neman amincewar majalisa dangane da dokar ta-baci, wanda za a karanta domin tattaunawa.

Kafin fara tattaunawar ne aka samu takaddama wanda hakan ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta a Najeriya.

A yanzu haka dai kallo ya koma kan yan majalisar domin ganin matakin da za su dauka a kan bukatar shugaban kasa ta sanya dokar ta-baci a jihar Rivers.

Kara karanta wannan

'Za a iya samun karamin yaki a Rivers,' 'Yan Neja Delta sun gargadi Tinubu

Matasa sun yi wa Shehu Sani rubdugu

A wani rahoton, kun ji cewa matasan Najeriya sun yi rudugu wa Sanata Shehu Sani kan goyon bayan matakin saka dokar ta baci da Bola Tinubu ya yi a Rivers.

Shehu Sani ya ce dokar ta-baci ce babbar mafita a kan halin da aka shiga a Rivers, domin a cewarsa an riga an bi sauran matakai amma an gaza samun mafita.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng