'Ba Ka ga komai ba a Siyasa': Wike Ya Gargadi Gwamna kan Hatsarin da Ke Nufo Shi
- Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce gwamna Siminalayi Fubara ya fadi siyasa kuma karin matsaloli na nan tafe a gare shi
- Wike ya zargi Fubara da yawo da mutanen da suka nemi zama gwamna, yana cewa ba su da niyyar alheri ga jihar Rivers
- Ya bayyana cewa bai amince da hadin gwiwar Fubara da wadancan mutane ba saboda bai yarda da su ba tun farko
- Wike ya ce ko an tsige Mai girma Fubara, babu wani hargitsi da zai biyo baya, domin tsarin kundin mulki ya tanadi hakan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya, Abuja kuma tsohon gwamnan Rivers, Nyesom Wike ya yi magana kan rigimar jihar.
Wike ya ce Gwamna Siminalayi Fubara tun yanzu ya fara rasa goyon baya a siyasa kuma bai ga komai ba ma tukuna.

Asali: Facebook
Wike ya magantu kan yiwuwar tsige Fubara
Wike ya fadi haka ne a wani taron girmamawa da mutanen Kalabari suka shirya a Abalama da ke Port Harcourt, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan ya biyo bayan kalaman Wike a makon da ya gabata cewa babu abin da zai faru ko an tsige gwamna Fubara daga kujerarsa.
A wata ganawa da manema labarai a Abuja, Wike ya ce babu abin mamaki idan majalisa ta tsige gwamna mai ci bisa doka.
Wike ya kara da cewa:
“Idan ka aikata laifin da ya cancanci tsige ka, me ke damun mutane? Shin laifi ne hakan?”
“In har ka karya kundin tsarin mulki kuma majalisa ta ga dacewar tsige ka, ai hakan ya na bisa doka.”
“Na ji wasu suna cewa, ‘idan an tsige shi, za a samu rikici’, wauta ce! ba za a ga wani rikici ba.”
Wike ya kuma ce ba gaskiya ba ne cewa majalisar tana aiki da mugun nufi, ya ce da ba haka ba, da sun yi hutu na watanni shida.

Asali: Facebook
Wike ya gargadi Fubara game da tasirin siyasarsa
Tsohon gwamnan ya soki zabin abokan tafiyar Fubara, yana cewa wadanda ke kewaye da shi sun taba neman kujerar gwamna a baya.
A cewarsa, ya ki amincewa da hadin gwiwar Fubara da wadannan mutane saboda sun kasance ba su da niyya mai kyau.
Wike ya ce Fubara ya riga ya fadi siyasa kuma karin koma baya na tafe a gare shi cikin lokaci nan kusa.
Ya ce:
“Kai (Fubara) kana tare da wadanda suka taba son kujerarka ta gwamna, na ce ba su da alheri ga jihar Rivers.
“Su ne suke ba ka shawara, amma me ka ke tsammani? Shawarwarinsu marasa kyau sun jefa ka cikin matsala.
“Ka riga ka fadi, kuma akwai koma baya da zai biyo baya, ban taba ganin irin wannan siyasa ba.”
An gargadi Tinubu kan rigimar Rivers
Kun ji cewa 'yan kalibar Ijaw sun yi barazanar ɗaukar matakin da zai ba Bola Tinubu mamaki idan ya sake aka tsige Gwamna Siminalayi Fubara.

Kara karanta wannan
An sake rikita Tinubu, Kwankwaso, Obi da gwamnonin PDP sun shirya raba shi da mulki
Wata kungiyar ƴan Ijaw, mai rajin kare al'adu ta bayyana cewa da sanin Tinubu ne Wike ya ke abin da ya ga dama a rikicin siyasar jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng