Bayan Ficewar El Rufai, Ganduje Ya Fadi Shirin APC Na Kwace Jihohi 2 a hannun PDP

Bayan Ficewar El Rufai, Ganduje Ya Fadi Shirin APC Na Kwace Jihohi 2 a hannun PDP

  • Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa suna da shiri na musamman kan jihohin Oyo da Osun
  • Ganduje ya bayyana cewa jam'iyyar APC na son ƙwato jihohin biyu na yankin Kudu maso Yamma daga hannun PDP mai hamayya
  • Shugaban na APC ya bayyana cewa za su yi aiki tuƙuru domin ganin cewa sun cimma burinsu na ƙwato jihohin a zaɓe mai zuwa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Oyo - Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi magana kan shirin jam'iyyar kan jihohin Oyo da Osun.

Ganduje ya bayyana cewa jam’iyyar APC mai mulki na da tsari da shiri na musamman domin ƙwace mulki daga jam’iyyar adawa ta PDP a jihohin Oyo da Osun.

Ganduje ya fadi shirin APC kan jihohin Oyo da Osun
Ganduje ya bayyana cewa APC za ta kwato jihohin Oyo da Osun Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Facebook

Ganduje ya bayyana hakan ne a ranar Laraba lokacin da ya karɓi Dr. Gbenga Adegbola, wanda ya koma jam’iyyar APC a hukumance, cewar rahoton jaridar Tribune.

Kara karanta wannan

El Rufai ya bayyana alfarmar da Shugaba Tinubu ya nema a wajensa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jihohin Oyo da Osun suna Kudu maso Yamma, wanda shi ne yankin shugaba Bola Tinubu.

Waɗanne jihohi APC ke son ƙwacewa a hannun PDP?

Ganduje ya jaddada cewa ƙwace waɗannan jihohi daga PDP zai tabbatar da abin da ya kira "siyasar bai ɗaya" ga APC a yankin.

"Tsarinmu na siyasa ga yankin Kudu maso Yamma a shekarar 2027 an laƙaba masa suna ‘siyasar bai ɗaya’."
"A takaice, bisa ga shirinmu, za mu yi aiki tuƙuru tare da taimakon Allah (SWT) da goyon bayan jama’a don tabbatar da cewa Oyo ta koma hannun APC a 2027."
"Haka nan kuma Osun, wacce ke hannun jam’iyyar adawa a yanzu, za ta koma jihar APC, Insha Allah. Wannan ne ma’anar siyasar bai ɗaya da muke nufi."

- Abdullahi Umar Ganduje

Abdullahi Ganduje ya yi maraba da shiga APC

Ganduje ya tabbatarwa Adegbola cewa jam’iyyar APC za ta ba shi cikakkiyar damar shiga cikin harkokinta a matsayinsa na mamba.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya tsage gaskiya shirtinsa na bin El Rufai zuwa SDP

"Muna maka maraba da dawowa cikin APC kuma muna tabbatar maka cewa yanzu kai cikakken mamba ne na jam’iyyarmu."
"Saboda haka, ka na da dama da ƴanci na tsayawa takara a kowane matsayi da ka ke so a cikin jam’iyyar."
"Idan ka yanke shawarar tsayawa takara a zaɓe, za mu tabbatar da cewa ka samu ingantacciyar dama da yanayi mai kyau don cin nasara."

- Abdullahi Umar Ganduje

Bayan ganawarsa da Ganduje da wasu shugabannin jam’iyyar APC na ƙasa, Adegbola ya bayyanawa manema labarai cewa yana da magoya baya sama da 10,000.

Ya kuma tabbatar da cewa zai yi aiki tare da sauran masu ruwa da tsaki a jihar Oyo domin ganin jam’iyyar ta samu nasara a babban zaɓe mai zuwa, musamman a zaɓen gwamna.

Ƴan majalisun adawa sun koma APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC ta samu ƙaruwa a jihar Edo bayan wasu ƴan majalisu huɗu na jam'iyyun adawa sun koma cikinta.

Kara karanta wannan

"Da shi muka shirya yaƙar Atiku," Wike ya tona asirin gwamna a Arewacin Najeriya

Ƴan majalisun da suka sauya sheƙar zuwa APC sun haɗa da gudu uku na jam'iyyar PDP da guda ɗaya na jam'iyyar LP.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng