APC Ta Fara Yakin Nemawa Tinubu Tazarce a Jihohin Arewa a 2027
- Kusan shekaru biyu kafin zaben 2027, wasu manyan ‘yan jam’iyyar APC sun fara kamfen don ganin Bola Ahmed Tinubu ya zarce a mulki
- Shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje da Sakataren Gwamnatin Tarayya sun bukaci ‘yan siyasar Arewa da ke son takara su hakura
- Wannan mataki ya jawo ce-ce-ku-ce daga ‘yan adawa da masu sharhi kan siyasa, inda wasu ke cewa hakan ya sabawa dokokin zabe
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja - Yayin da wa’adin mulkin Bola Ahmed Tinubu bai kai shekaru biyu ba, wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar APC sun fara kokarin tabbatar da sake zabensa a 2027.
Duk da cewa ba a fara yakin neman zabe ba a hukumance, shugabannin APC irin su Abdullahi Ganduje da George Akume sun bukaci ‘yan takarar Arewa su dakata har zuwa 2031.

Asali: Twitter
Kamfen din Tinubu ya bazu a Arewa
Daily Trust ta hada rahoto kan matakan da 'yan APC suka fara dauka domin ganin Tinubu ya samu goyon baya a jihohin Arewa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wani taro da Ganduje ya jagoranta a hedikwatar APC a Abuja, ya bukaci ‘yan siyasar Arewa da ke da burin shugabancin kasa su hakura har sai bayan Tinubu ya kammala wa’adinsa na biyu.
Wasu daga cikin jihohin da aka fara yakin neman zabe a ciki sun hada da Kaduna, Kebbi da Kwara. Haka nan an fara ganin hotunan Tinubu a wasu wurare a Abuja, babban birnin tarayya.
A watan da ya gabata, APC ta shirya gangamin siyasa a jihar Kebbi domin yakin neman zaben Tinubu da kuma gwamna Nasir Idris.
Taron wanda aka gudanar a filin wasa na Birnin Kebbi, ya samu halartar manyan shugabanni kamar su Ministan Kasafin Kudi, Atiku Bagudu, da Hon. James Abiodun Faleke.
Bagudu ya bayyana cewa Tinubu ya cancanci zarcewa, yana mai cewa:
“Gwamnatin Tinubu ta yi kokari sosai wajen inganta Najeriya. Ya cika alkawuran da ya dauka ga mutanen Kebbi.”
Haka kuma gwamnan Kebbi, Nasir Idris ya ce jama’ar jihar suna tare da Tinubu saboda irin ci gaban da ya kawo musu.
Masu sharhi sun soki kamfen da aka fara
Masana dokoki da ‘yan adawa a Najeriya sun soki wannan mataki, suna masu cewa hakan ya sabawa doka.
Sun bayyana cewa sashe na 94 (1) na Dokar Zabe ta 2022 ya tanadi cewa yakin neman zabe ba zai fara ba sai kwanaki 150 kafin ranar zabe.
A cewar wasu masana, irin wadannan yakin neman zabe tun kafin lokaci na iya jawo rudani a siyasa da kuma tauye tsarin dimokuradiyya.
2027: Fara kamfen a Kaduna da Kwara
Wasu jiga-jigan APC irin su mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, da sakataren APC na kasa, Ajibola Basiru, sun goyi bayan sake zaben Tinubu yayin wani taro a jihar Kwara.

Kara karanta wannan
Bola Tinubu ya ware sama da Naira biliyan 700 a watan azumi, za a yi muhimman ayyuka
Haka kuma, ‘yan jam’iyyar APC a Kaduna sun nuna goyon bayansu ga Tinubu da gwamna Uba Sani, suka kada kuri’ar amincewa da su.
A wani taro da Ganduje da Sanata Barau suka shirya, wasu magoya bayan Atiku daga Arewa sun sauya sheka zuwa APC, suka sha alwashin yin aiki domin ganin Tinubu ya zarce a 2027.

Asali: Facebook
El-Rufa'i ya ziyarci Atiku Abubakar
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya ziyarci Atiku Abubakar wanda wannan shi ne karo na biyu.
Atiku Abubakar ya karbi Nasir El-Rufa'i ne a gidansa yayin da ake shirin buda baki bayan kammala azumin rana ta tara a watan Ramadan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng