Lissafi Zai Koma Sabo a APC, Ahmad Lawan Zai Iya Shiga Takarar Majalisar Dattawa

Lissafi Zai Koma Sabo a APC, Ahmad Lawan Zai Iya Shiga Takarar Majalisar Dattawa

  • Ana kishin-kishin cewa Ahmad Ibrahim Lawan zai so ya zarce a kan kujerarsa a Majalisar dattawa
  • Rabuwar da aka samu tsakanin jam’iyyar APC ya jawo shugaban majalisar zai nemi ya sake yin takara
  • Shugabannin APC sun ware kujerar majalisa zuwa Kudu, an tsaida Godswill Akpabio/Jibrin Barau

Abuja - Akwai yiwuwar takarar shugabancin majalisar dattawa ta zama tsakanin mutane uku domin abubuwa su na neman canzawa.

Rahoto na yawo cewa shugaban majalisar dattawa mai-ci watau Dr. Ahmad Ibrahim Lawan ya na so ya shiga takarar da za ayi wannan karo.

Sanata Ahmad Ibrahim Lawan ya yi nasarar dawowa majalisa duk da ya nemi tikitin takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar APC.

AHmad Lawan
Shugaban Majalisar Dattawa Hoto: Ahmad Lawan / Tope Brown
Asali: Facebook

Bayan an yi ta shari’a a kotu, Lawan ya doke Bashir Sheriff Machina domin wakiltar Arewacin Yobe a majalisar dattawa a karo na shida.

Kara karanta wannan

Bangarori 7 da Ake Jiran Bola Tinubu Ya Kawo Gyara Idan Ya Gaji Muhammadu Buhari

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Idan Shugaban majalisar ya shiga takarar da za ayi a Yuni, za a samu akalla Sanatoci uku da ke neman kujera ta uku a daraja a dokar kasa.

Akwai tsagin Godswill Akpabio/Jibrin Barau wanda jam’iyyar APC ta ayyana, sannan akwai masu tallata Orji Uzor Kalu/Abdulaziz Yari.

Wa zai canji tikitin Ovie Omo Agege?

Mataimakin shugaban majalisar dattawa mai barin-gado watau Ovie Omo Agege bai nemi tazarce ba, ya yi takarar Gwamna ne a jihar Delta.

Wata majiya ta ce Dr. Lawan ya shirya mutanen da za su taya shi kamfe kuma akwai yiwuwar ya sake neman kujerarsa tare da Osita Isunaso.

Osita Isunaso shi ne Sanatan da zai wakilci Imo ta yamma a majalisar dattawa, kuma ya na cikin wadanda su ka nuna sha’awar samun mukami.

Rahoton ya ce Lawan ya na tare da Sanatoci irinsu Ifeanyi Ubah da Sani Musa, kuma yana da goyon bayan Hope Uzodinma da Cif Emeka Offor.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Yadda ’Yan Majalisu Ke Raba Daloli Don Neman Goyon Bayan a Zabe Su

Babu ruwa na - Sanata

Gwamnan jihar Imo, Uzodinma ya na cikin masu fada a ji a APC daga Kudu maso gabas. Amma Sanata Sani Musa ya musanya rade-radin.

Sun ta rahoto Sanatan na Neja ya na cewa bai da hannu a zargin yunkurin goyon bayan Lawan ya rike kujerarsa, ya ce bai canza matsaya ba.

Biden zai aiko wakilai Najeriya

Joe Biden ya bar Atiku Abubakar da Peter Obi da guna-guni, domin an ji labari zai aiko da wakilai zuwa Najeriya domin zuwa bikin rantsar da Bola Tinubu.

Sanarwa ta fito daga White House cewa Marcia L. Fudge za ta jagoranci tagawar Shugaban Amurka. A cikin 'yan tawagar da za a tura akwai Enoh T. Ebong.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel