Kaduna: Jam’iyyar APC Na Shirin Dakatar da Nasir El-Rufai? Gaskiya Ta Bayyana

Kaduna: Jam’iyyar APC Na Shirin Dakatar da Nasir El-Rufai? Gaskiya Ta Bayyana

  • Game da rahotannin da ake yadawa na cewar jam'iyyar APC na shirin dakatar da Nasir El-Rufai, kakakin jam'iyyar na Kaduna ya magantu
  • Salisu Wusono, a ranar Talata ya bayyana cewa babu wani shiri na dakatar da El-Rufai, tsohon gwamnan jihar daga jam'iyyar
  • A baya-bayan nan ne rahotanni suka rika yawo na cewa APC za ta sallami El-Rufai saboda wasu ayyuka na zagon kasa da yake yi a kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kaduna - Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Kaduna ta ce babu wani shiri na dakatar da Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan jihar.

Jam'iyyar APC a KAduna ta magantu kan dakatar da Nasir El-Rufai
APC ta ce babu wani shiri a kasa na dakatar da tsohon gwamnan Kaduna, El-Rufai. Hoto: @elrufai
Asali: Facebook

An samu rahotannin cewa nan ba da jimawa ba za a dakatar da El-Rufai bisa zargin yin ayyukan da suka sabawa jam’iyya.

Kara karanta wannan

Binciken El-Rufai: An bayyana dalilin kafa kwamitin bin diddikin ayyukan tsohon gwamnan

A wani sako da ya aikawa jaridar TheCable a daren ranar Talata, Salisu Wusono, kakakin jam’iyyar APC a Kaduna, ya ce APC ba ta shirya hakan ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Babu wannan maganar!" a cewar Wusono.

Wadanne ayyuka ne El-Rufai ya aikata?

A kwanakin baya ne aka ga El-Rufai tare da Abdul Ningi, sanatan da aka dakatar da shi bayan yayi zargin cewa an yi cushe a kasafin kudin shekarar 2024.

Haka kuma jaridar Legit Hausa ta rahoto El-Rufai ya kuma ziyarci hedikwatar jam’iyyar adawa ta Social Democratic Party (SDP) da ke Abuja.

Wadannan ziyarce-ziyarcen sun haifar da cece-kuce a shafukan sada zumunta, a daidai lokacin da ake ta yada jita-jitar cewa tsohon gwamnan na shirin sauya sheka.

El-Rufai ya ziyarci Borno

Ba a wani jima ba kuma sai aka ga tsohon gwammnan na Kaduna ya dura Maiduguri, babban birnin jihar Borno, inda ya gana da Gwamna Babagana Umara Zulum.

Kara karanta wannan

Atiku vs Wike: An yi hasashen abin da zai faru a wajen taron NEC na PDP

A yayin ziyarar, El-Rufai ya yi magana a wani taron karawa juna sani wanda jihar ta shirya, inda ya fallasa gwamnatin Tinubu kan dawo da biyan tallafin fetur.

Har ila yau, a taron ne tsohon gwamnan ya kuma tona asirin yadda wasu gwamnoni ke amfani da wata dabara ta tafka magudin zabe a jihohinsu.

Majalisar Kaduna za ta binciki El-Rufai

Tun da fari, Legit Hausa ta rahoto yadda majalisar jihar Kaduna ta kafa wani kwamiti wanda zai binciki basussuka, kudin tallafi da yadda Nasir El-Rufai ya tafiyar da mulkin jihar.

Kwamitin zai yi duba kan yadda aka karbo kudaden da yadda aka kashe su, da ma tuhumar wani na hannun daman El-Rufai wanda ake zarginsa da almundahana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel