El-Rufai Ya Shiga Sabuwar Matsala Yayin da Majalisar Kaduna Ta Kafa Kwamitin Bincike

El-Rufai Ya Shiga Sabuwar Matsala Yayin da Majalisar Kaduna Ta Kafa Kwamitin Bincike

  • Majalisar dokokin jihar Kaduna ta kafa wani kwamiti da zai binciki yadda Malam Nasir El-Rufai ya tafiyar da mulkin jihar daga 2015 zuwa 2023
  • Haka zalika kwamitin zai yi duba kan basussukan da tsohuwar gwamnatin ta karbo, kudaden tallafi da ta fitar da yadda ta gudanar da ayyuka
  • Wannan na zuwa ne bayan da gwamnan jihar na yanzu, Uba Sani ya zargi El-Rufai da karbo tulin bashi a lokacin da yake gwamna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kaduna - Majalisar dokokin jihar Kaduna ta kafa wani kwamiti da zai binciki yadda aka tafiyar da mulkin jihar karkashin tsohon gwamna Nasir El-Rufai.

An dora wa kwamitin alhakin duba kudaden lamuni, tallafi, da yadda aka aiwatar da ayyuka daga 2015 zuwa 2023 lokacin da El-Rufai ke rike da jihar, jaridar The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tsoffin gwamnoni 4 da sanatocin Arewa 8 a Majalisa da ba su gabatar da kudiri ba a watanni 10

Majalisar Kaduna za ta binciki gwamnatin El-Rufai
Kwamiti zai duba kudaden lamuni, tallafi, da yadda aka aiwatar da ayyuka daga 2015 zuwa 2023. Hoto: @elrufai
Asali: Facebook

An zargi El-Rufai ta tara bashi

A ranar 30 ga Maris, Uba Sani, gwamnan Kaduna, ya ce gwamnatinsa ta gaji bashin dala miliyan 587, da Naira biliyan 85, da kuma bashin kwangiloli 115 daga gwamnatin El-Rufai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake magana a yayin wani taro na jama'a, Sani ya ce bai aro ko kobo ba a cikin watanni tara da suka gabata ba.

Ya ce, tulin bashin da gwamnatin El-Rufai ta bari yana cin kaso mai tsoka na kudin da jihar ke samu daga rabon tarayya na wata-wata.

El-Rufai: Wadanda kwamitin zai gayyata

Sai dai a ranar Talata, majalisar ta kafa kwamitin da niyyar zai kuma binciki babban hadimin tsohon gwamnan kuma babban mai ba da shawara kan harkokin zuba jari, Jimi Lawal.

Jaridar The Punch ta rahoto majalisar ta kuma umarci kwamitin da ya gayyaci fitattun mutane da suka hada da tsoffin shugabannin majalisar ta takwas da ta tara domin yi masu tambayoyi.

Kara karanta wannan

Malam El-Rufai ya faɗi Ministoci da Hadiman da ya kamata Tinubu ya kora daga aiki

Sauran sun hada da kwamishinonin kudi, tsoffin daraktocin kasuwannin Kaduna, da kwamishinonin kasafin kudi da tsare-tsare da dai sauransu.

Wahalar da ke tunkarar Najeriya - Ayodele

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa Primate Ayodele, shugaban cocin INRI Evangelical, ya aika sakon gaggawa ga shugaban kasa Bola Tinubu kan tattalin arziki.

Ayodele ya ce akwai wahalar rayuwa da ya hango na tunkarar kasar kuma 'yan Najeriya za su fuskanci tsadar kayayyaki da ta nunka ta yanzu ma damar gwamnati ba ta dauki mataki ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel