Majalisar Kano Ta Ɗauki Mataki Kan Ɗan Kwankwaso da Mutum 3 da Gwamna Yusuf Ya Naɗa

Majalisar Kano Ta Ɗauki Mataki Kan Ɗan Kwankwaso da Mutum 3 da Gwamna Yusuf Ya Naɗa

  • Majalisar dokokin jihar Kano ta tabbatar da naɗin ɗan Kwankwaso da wasu mutum uku a matsayin sababbin kwamishinoni
  • Shugaban majalisar, Isma'il Falgore, ne ya jagoranci tantance kwamishinonin a zaman majalisar na ranar Talata a Kano
  • Tun a farko, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tura sunayen mutum 4 da ya naɗa a kwamishinoni da kuma sabbin ma'aikatun da ya ƙirƙiro

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Majalisar dokokin jihar Kano ta tantance tare da tabbatar da naɗin sababbin kwamishinoni huɗu waɗanda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya miƙa mata.

Majalisar ta tantance kwamishinonin ne a zamanta na ranar Talata, 2 ga watan Afrilu, 2024, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ramadan: Murna yayin da aka fara rabon tallafin Ɗangote a jihohin Najeriya, Kano ce farko

Gwamna Yusuf da ɗan Kwankwaso.
Sababbin kwamishinonin Kano sun tsallake matakin tantancewa a majalisa Hoto: Abba Kabir Yusuf, Mustapha Rabiu Kwankwaso
Asali: Twitter

A ƙarshen zaman ranar Talata ne majalisar ta ayyana shiga zaman kwamitin da ya ƙunshi mambobin majalisar gaba ɗaya domin tantance waɗanda gwamna ya naɗa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jerin sunayen sababbin kwamishinoni 4

Daga cikin waɗanda majalisar da tantance har da Mustafa Rabi’u- Kwankwaso, ɗan tsohon gwamnan Kano kuma jagoran jam'iyyar NNPP na ƙasa, Rabi'u Musa Kwankwaso.

Sauran mutane ukun sune, Adamu Aliyu-Kibiya, Abduljabar Garko, da kuma Shehu Aliyu-Yanmedi.

Bayan kammala tantance su ne sai shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawan Hussaini (NNPP-Dala) ya gabatar da kudirin tabbatar da sababbin kwamishinonin.

Labaran Madari (APC-Warawa), shugaban marasa rinjaye na majalisar dokokin Kano ne ya goyi bayan kudirin tabbatar da naɗin mutanen.

Majalisa ta amince da buƙatar Gwamna

Kakakin majalisar, Ismail Falgore (NNPP-Rogo), bayan kada kuri’ar amincewa da kudirin, ya tabbatar da wadanda aka tantance sannan ya umurci magatakarda ya tura matakin majalisa zuwa ofishin gwamna.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya ɗauko ɗan Arewa, ya naɗa shi a babban muƙami a watan azumi

A ranar 26 ga watan Maris ne Gwamna Yusuf ya mika jerin sunayen sababbin kwamishinoni hudu da sabbin ma’aikatu hudu da gwamnatin ta kirkira, rahoton Vanguard.

Sababbin ma’aikatun dai sun hada da ma’aikatar jin kai, ma’aikatar wutar lantarki da makamashi, ma’aikatar tsaron cikin gida, da ma’aikatar ma’adanai.

Sanatoci na shirin tsige Akpabio?

A wani rahoton na daban Majalisar dattawa ta bayyana gaskiya kan raɗe-raɗin cewa sanatoci na shirin tsige Sanata Akpabio daga shugabancin majalisar.

Rahotanni sun nuna cewa sanatoci sun ɗauki zafi kuma har sun fara kulle-ƙullen yadda za su sauke Akpabio daga kujerar shugaban majalisar dattawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel