Sanatoci Sun Fara Sabon Shirin Tsige Shugaban Majalisar Dattawa? Bayanai Sun Fito

Sanatoci Sun Fara Sabon Shirin Tsige Shugaban Majalisar Dattawa? Bayanai Sun Fito

  • Majalisar dattawa ta bayyana gaskiya kan raɗe-raɗin cewa sanatoci na shirin tsige Sanata Akpabio daga shugabancin majalisar
  • Rahotanni sun nuna cewa sanatoci sun ɗauki zafi kuma har sun fara kulle-ƙullen yadda za su sauke Akpabio daga kujerar shugaban majalisar dattawa
  • Sanata Diket Plang ya musanta rahoton wanda ya kira da karya, inda ya ce an zaɓi Akpabio ne bisa la'akari da wasu ƙa'idoji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Sanata Diket Plang ya musanta raɗe-raɗin da ke yawo cewa sanatoci sun fara shirin tsige shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, daga kujerarsa.

Plang, wanda shi ne shugaban kwamitin kwadago kuma mataimakin shugaban kwamitin ɗa'a a majalisar dattawa, ya ce babu wani abu mai kama da tsige Akpabio.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya fadi abin da zai hana Tinubu yin shekara 8 kan karagar mulki

Sanata Godswill Akpbio.
Majalisar dattawa ba ta da shirin tsige Akpabio Hoto: NGRSenate
Asali: Facebook

Ya kuma yi nuni da yadda aka zaɓi Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa, inda ya ce sai da aka duba abin da ƴan Najeriya suke kauna kafin zaɓensa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Plang ya yi wannan bayanin ne yayin da yake zantawa da ƴan jarida a Jos, babban birnin jihar Filato, kamar yadda Tribune Nigeria ta ruwaito.

Yadda aka raba manyan kujerun siyasa

Ya kuma ƙara da cewa duk wata kujera a matakin ƙasa da aka zaɓa sai da aka yi la'akari da dukkan shiyyoyin ƙasar nan guda shida, cewar Premium Times.

A kalamansa, sanatan ya ce:

"Babu wanda zai tsige Shugaban Majalisar Dattawa, yana nan daram a kan kujerarsa, mu muka zaɓe shi kuma sai da aka duba abubuwa da dama yayin zaɓensa.
"Arewa maso Yamma ta samu mataimakin shugaban majalisar dattawa, Arewa maso Gabas tana da mataimakin shugaban ƙasa, Arewa ta Tsakiya an ba ta sakataren gwamnati, ita kuma kudu ta samu shugaban majalisar dattawa.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Miyagu sun kutsa kai har ofis, sun kashe babban malamin jami'ar Arewa

"Wadannan ma'aunai aka yi domin daidaito. Ina so in tabbatar muku da cewa majalisar dattawa ta 10 majalisa ce ta jama’a kuma ta mayar da hankali kan ayyukan da suka rataya a kanta.

Gwamnati za ta yarda a tsige Akpabio?

Sanatan ya ce babu wani ɓangare a ƙasar nan da zai sauya tsarin, inda ya ce jita-jitar da ake cewa sanatocin Arewa ba su kaunar Akpabio ba gaskiya bane.

A cewarsa, gwamnatin tarayya a ƙarƙashin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ba za ta bari a tsige Akpabio ba.

Ƴan Arewa za su dakatar da Tinubu?

A wani rahoton kuma Kungiyar Arewa ta bayyana cewa babu dalilin da zai sa ƴan Arewa su hana Bola Ahmed Tinubu yin tazarce zuwa zango na biyu a 2027.

Arewa Think Tank ta faɗi haka ne jim kadan bayan kammala taron addu'o'in da ta shiryawa Tinubu na cika shekaru 72 a jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel