Abba Ya Aika Wa Majalisar Kano Muhimmiyar Buƙata, Zai Kafa Sababbin Ma’aikatu

Abba Ya Aika Wa Majalisar Kano Muhimmiyar Buƙata, Zai Kafa Sababbin Ma’aikatu

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aika wa majalisar jihar Kano bukatar kafa sababbin ma'aikatu guda hudu domin ci gaban jihar
  • Ma'aikatun ayyukan jin kai, wutar lantarki da makamashi, tsaron cikin gida, da kuma ma’adanai su ne Abba ke so a kirkira
  • Yusuf ya kuma mika sunayen mutane hudu ga majalisar domin tantance su a matsayin mambobi a majalisar zartarwa ta jiha

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf ya rubutawa majalisar dokokin jihar takardar neman amincewar kafa sababbin ma’aikatu hudu.

Abba ya aika wa majalisar Kano bukatar kafa sabbin ma'aikatu
Gwamna Abba Yusuf na shirin kirkirar sabbin ma'aikatu hudu a Kano. Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

Jerin ma'aikatun da Abba zai kirkira

Gwamnan, a cikin wasikar da kakakin majalisar Jibrin Falgore ya karanta, ya nemi a amincewar kafa sabbin ma’aikatun domin ci gaban jihar Kano.

Kara karanta wannan

Kano: Abba Kabir ya tura sunan ɗan Kwankwaso da mutum 3 Majalisa domin tantancewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Falgore ya ce ma’aikatun da ake son a samar sun hada da ma'aikatar ayyukan jin kai, wutar lantarki da makamashi, tsaron cikin gida, da kuma ma’adanai.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Gwamna Yusuf ya kuma bukaci amincewar majalisar wajen rusa shuwagabannin hukumar majalisar jihar da nada sabbin mambobi.

Abba zai nada sabbin kwamishinoni

Sababbin mambobin za su hada da tsohon kakakin majalisar, Gambo Sallau a matsayin shugaba, Zubairu Mamuda, Al’asan Kibiya, Ali Bala da kuma Halima Uba Jalli.

Sauran sun hada da Surajo Danbatta, Yahaya Rogo, Abubakar Dala da Garba Tsanyawa.

Rahoton jaridar The Punch ya nuna cewa Yusuf ya mika sunayen mutane hudu ga majalisar domin tantance su a matsayin kwamishinoni.

Wadanda mika sunayensu domin nadin sune Adamu Kibiya, Abdujjabbar Garko, Shehu Karaye da Mustafa Rabi’u-Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Mambila: An tona yadda aka nemi amfani da kaidin mata a yaudari wasu ministoci

Abba ya nada dan Rabiu Kwankwaso?

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa Gwamn Abba Yusuf, ya zabi dan ubangidansa a siyasa kuma tsohon gwamnan jihar, Rabiu Kwankwaso, a matsayin kwamishina.

Yusuf ya gabatar da sunan Mustapha Kwankwaso da wasu mutane uku a gaban majalisar dokokin jihar a ranar Talata domin tantance su a matsayin mambobin majalisarsa.

Tsohon kwamishinan filaye da tsare-tsare, Adamu Aliyu, wanda aka kora a watan Satumba saboda ya yi barazanar kisa ga alkalan kotun zaben jihar na cikin wadanda aka zaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel