Ramadan: Murna Yayin da Aka Fara Rabon Tallafin Ɗangote a Jihohin Najeriya, Kano Ce Farko

Ramadan: Murna Yayin da Aka Fara Rabon Tallafin Ɗangote a Jihohin Najeriya, Kano Ce Farko

  • Alhaji Aliko Ɗangote ya fara ɗaukar matakan rage wa masu karamin ƙarfi raɗadin wannan matsin tattalin arziki da aka shiga a Najeriya
  • Attajirin ɗan kasuwar ya fara rabon buhunan shinkafa 120,000 ga al'ummar jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya
  • Da yake mayar da martani, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yabawa attajirin inda ya ce hakan abu ne mai kyau a irin lokacin da ake ciki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote Group, Alhaji Aliko Ɗangote, ya fara shirin tallafawa talakawa marasa galihu da kayan abinci a faɗin ƙasar nan.

Attajirin ya ɗauki wannan matakin ne domin ba da gudummuwarsa a yunkurin daƙile wahalhalun matsin tattalin arziƙi a Najeriya.

Kara karanta wannan

Fitaccen malamin addini a Arewa ya tona manyan mutanen da ke haɗa kai da ƴan bindiga

Abba da Ɗangote.
Ramadan: Gwamna Abba ya yi farin ciki yayin da Ɗangote ya raba buhunan shinkafa a Kano Hoto: Kano State Government
Asali: Twitter

Ɗangote zai fara da mutum miliyam ɗaya waɗanda za su ci gajiyar tallafin buhun shinkafa mai nauyin kilo 10 kowanensu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fitaccen ɗan kasuwan ya fara rabon tallafin ne a mahaifarsa jihar Kano, inda za a raba buhunan shinkafa 120,000 domin rage wa marasa galihu raɗaɗin halin ƙuncin da suke ciki.

A cewar Dangote, an yi hakan ne domin magance matsalolin da marasa galihu ke fuskanta a watan Ramadan, kamar yadda TVC News ta ruwaito.

Yadda za a raba tallafin Ɗangote a Kano

Ɗangote ya bayyana cewa rukunin farko na rabon ya ƙunshi mutum miliyan ɗaya da zasu ci gajiya kuma kowane mutum ɗaya za a ba shi buhun shinkafa mai nauyin kilo 10.

Daga cikin mutane miliyan daya da zasu ci gajiyar tallafin a Najeriya, jihar Kano ta karbi 120,000 a wani biki da gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf ya shirya a gidan gwamnati.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya shiga sabuwar matsala kan zargin alaƙa da ƴan bindiga, bayanai sun fito

Gwamma Yusuf ya mayar da martani

Da yake mayar da martani, Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano, ya yaba da karamcin Dangote.

Ya ce rabon kayayyakin ya zo ne a daidai lokacin da mutane da dama ke cikin tsananin bukatar agaji.

A cewarsa, rabon tallafin zai rage yunwa da kuma taimakawa wajen samar da mafita na dogon lokaci ga mutane masu ɗumbin yawa a fadin Najeriya.

Tinubu ya saka tallafi a hajjin 2024

A wani rahoton kuma Gwamnatin tarayya ƙarƙashin Bola Tinubu ta tallafawa aikin hajjin bana da N90bn domin ragewa alhazai tsadar kuɗin kujera.

Wata majiya daga hukumar NAHCON ta bayyana cewa wannan tallafin ne ya sa aka nemi alhazai su cika N1.9m amma da sai ƙarin ya wuce haka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel