Wata Sabuwa: Gwamnan PDP Ya Naɗa Tsohon Shugaban Tsageru a Matsayin Sarki Mai Martaba

Wata Sabuwa: Gwamnan PDP Ya Naɗa Tsohon Shugaban Tsageru a Matsayin Sarki Mai Martaba

  • Gwamna Simo Fubara ya ɗaga darajar tsohon shugaban tsageru zuwa matakin Sarki mai daraja ta farko a jihar Ribas
  • Siminalayi Fubara ya mika takardar shaida da sandar mulki ga Amanyanabo na masarautar Okochiri, Sarki Ateke Michael Tom
  • Ya ce ya ɗauki wannan matakin ne duba da namijin ƙoƙarin da yake yi wajen tabbatar da zaman lafiya a yankinsa da jihar gaba ɗaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ribas - Gwamna Siminalayi Fubara a ranar Talata ya ba da takardar shaidar karramawa da sandar mulki ga Amanyanabo na masarautar Okochiri, Sarki Ateke Michael Tom.

Wannan na nufin gwamnan ya ɗaga darajar Sarkin zuwa matakin basarake na matakin farko a jihar Ribas, kamar yadda PM News ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An yi garkuwa da matar Gwamnan PDP bayan musayar wuta? Gaskiya ta bayyana

Gwamna Fubara na jihar Ribas.
Tsohon shugaban tsageru ya zama Sarki mai daraja ta ɗaya a Ribas Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Twitter

Gwamna Fubara ya miƙa abubuwan da ke nuna ya amince da tsohon shugaban tsagerun a matsayin basaraken gargajiya mai daraja ta farko a Ribas a gidan gwamnati a Fatakwal.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da Fubara ya faɗawa Sarkin

Da yake jawabi yayin taron, Fubara ya yi kira ga Ateke Tom da ya kasance daya daga cikin wadanda za su ceci jihar.

"Muna kan wani siraɗi da ake buƙatar dukkanmu mu tsaya kan gaskiya, hakan ya kan faru sau ɗaya a rayuwa, don haka ina so ka zama ɗaya daga cikin waɗanda za su ceto jiharmu da muke ƙauna.
"Kuma na san cewa tun da muka samu goyon bayan Amanyanabo na Okochiri, tare da goyon bayan majalisar Sarakuna da goyon bayan al’ummar jihar Ribas, za mu yi nasarar kawo zaman lafiya a jihar nan.
"Za mu ci gaba da tuntuba, ba za mu yi mulkin kama-karya ba. Mun san cewa wata rana zamu sauka, idan muka bar gadon mulki aikin mu zai nuna su waye mu. Ba wanda zamu tilasta ya faɗi magana mai kyau a kan mu."

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya faɗi Abu 1 da ya sa ƴan ta'adda suka daina kai hari makarantu a jiharsa

- Siminalayi Fubara.

Meyasa Fubara ya ɗaga darajar basaraken?

Gwamna Fubara ya yi bayanin cewa ya yi aiki ne a bisa ka’idar doka wajen ɗaga darajar kujerar sarautar da Sarki Ateke Tom ke zaune a kai zuwa matakin daraja ta farko.

A cewarsa, ya yi haka ne duba da ƙoƙarin da yake yi na samar da zaman lafiya a yankin Okrika da kuma jihar Ribas baki ɗaya, rahoton The Sun.

Tinubu ya ƙwace kwamishinan Fubara

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya ɗauke kwamishinan ayyukan jihar Ribas bayan ya naɗa shi a matsayin shugaban hukumar BCDA.

Dakta George-Kelly Alabo ya yi murabus daga mukamin kwamishinan ayyuka a gwamnatin Fubara saboda naɗin da Tinubu ya masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel