Gwamnan Sani Ya Ɗauki Nauyin Karatun Ɗaliban Kuriga da Aka Ceto Daga Hannun Ƴan Bindiga

Gwamnan Sani Ya Ɗauki Nauyin Karatun Ɗaliban Kuriga da Aka Ceto Daga Hannun Ƴan Bindiga

  • Malam Uba Sani ya ɗauki nauyin karatun ɗaliban makarantar Kuriga da aka ceto daga hannun ƴan bindiga ƙarƙashin gidauniyarsa
  • Gwamnan Kaduna ya kuma ɗauki alkawarin sabunta makarantar firamare da sakandiren gwamnati da ke Kuriga a ƙaramar hukumar Chikun
  • Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Sani ya jagoranci miƙa ɗaliban ga iyayensu kwanaki kusan uku bayan sojoji sun kuɓutar da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya yi tayin ɗaukar nauyin karatun dukkan ɗaliban makarantar kauyen Kuriga da aka ceto daga hannun ƴan bindiga.

Gwamna Sani ya ce zai ɗauki nauyin karatun ɗaliban ne ƙarƙashin gidauniyarsa wadda ta shafe shekaru 16, kamar yadda Channels tv ta ruwaito ranar Alhamis, 28 ga watan Maris, 2024.

Kara karanta wannan

An kashe manyan hatsabiban ƴan bindiga 2 da suka addabi bayin Allah a jihar Arewa

Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani.
Gudauniyar Uba Sani za ta ɗauki nauyin karatun ɗaliban Kuriga Hoto: Senator Uba Sani
Asali: Facebook

Malam Uba Sani ya kuma ɗauki alkawarin sake gina makarantar firamare da makarantar sakandiren gwamnati da ke Kuriga a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Waɗannan dai wani ƙari ne daga alƙawarin gwamnan na samar da kayayyakin more rayuwa a kauyen, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Gwamnan ya yi wannan furuci ne yayin da yake jawabi ga ɗaliban a gidan gwamnatin jihar Kaduna gabanin su kama hanyar komawa gida ƙauyen Kuriga.

Ayyukan da Uba Sani zai yi a Kuriga

Ya tabbatar masu da cewa matsalar garkuwa da mutane ba za ta hana su karatu ba, inda ya kara da cewa an tsaurara matakan tsaro a kauyen domin jama'a su ci gaba da harkokinsu.

Ya kuma sanar da bayar da gudummawar N10m ga iyalan malamin makarantar da ya mutu a hannun ƴan ta'adda, Abubakar Isah, tare da ɗaukar nauyin karatun ‘ya’yansa har zuwa jami’a.

Kara karanta wannan

Fitaccen malamin addini a Arewa ya tona manyan mutanen da ke haɗa kai da ƴan bindiga

"Yau za su koma gida da yardar Allah SWT, kuma ina son sanar da ku cewa dukkan ɗalibai 137, kamar yadda na yi musu alkawari, za su zama dalibai na da yardar Allah.
"Na riga na umarci gidauniyar Uba Sani wanda ta shafe shekaru 16 tana ba da ilimi da kiwon lafiya kyauta, ta ɗauki nauyinsu.
"Na kuma ba da umarnin cewa a yi gyare-gyare da dama a cikin kauyen da makarantun domin a ganina al’ummar Kuriga na daya daga cikin mutane masu son zaman lafiya a jihar Kaduna."

- Inji Uba Sani.

Uba Sani ya waiwayi Tudun Biri

A wani rahoton kuma watanni bayan kuskuren jefa bam kan ƴan Maulidi, Malam Uba Sani ya fara cika alƙawurran da ya ɗaukar wa kauyen Tudun Biri.

A watan Disamba ne sojoji suka jefa bam kan masulmi a taron Maulidi a kauyen, lamarin da ya yi ajalin mutane sama da 150.

Asali: Legit.ng

Online view pixel