Shugaba Bola Tinubu Ya Fara Shirin Ƙorar Wasu Ministoci Daga Aiki, Ya Jero Matakai 3

Shugaba Bola Tinubu Ya Fara Shirin Ƙorar Wasu Ministoci Daga Aiki, Ya Jero Matakai 3

  • Sabuwar matsala ta kunno kai ga ministocin da ke karkashin gwamnatin Bola Tinubu wadanda ba su aiwatar da aikin da aka dora masu ba
  • Wasu majiyoyi daga fadar shugaban ƙasa sun bayyana cewa shugaban na shirin rabuwa da dukkan ministocin da suka gaza taɓuka komai
  • Sun ce Shugaba Tinubu na shirin buɗe shafin yanar gizo da zai ba ƴan Najeriya damar faɗin ra'ayoyinsu da tantance ayyukan ministocin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

State House, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na shirin fara wani tsari mai matakai uku domin tantance ƙoƙarin ministoci, shugabannin ma’aikatu da hukumomin gwamnati.

Manufar ita ce samar da wani shafi da zai ba jama'a damar yin bayanai game da ƙoƙarin ministocin da ba da shawarin waɗanda za a rike da wadanda za a kora.

Kara karanta wannan

Okuama: Bola Tinubu ya gana da gwamnan PDP kan kisan sojoji 17, sahihan bayanai sun fito

Shugaban Kasa, Bola Tinubu.
An fara aikin tantance kokarin ministoci a mulkin Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Wannan yunƙuri na zuwa ne yayin da Gwamnatin Tinubu ke tunkarar bikin cika shekara ɗaya a kan madafun iko ranar 29 ga watan Mayu, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ruwayar Bussiness Day, wasu majiyoyi masu ƙarfi a fadar shugaban ƙasa sun ce Shugaba Tinubu zai kaddamar da wannan shafi ranar Talata (yau), 19 ga watan Maris.

A cewar majiyoyin wannan shafi zai ba ƴan Najeriya damar faɗin ra'ayoyinsu kan ayyukan ministoci da kuma koƙarin da suka yi, rahoton Naija News.

Sai dai an ɗaga buɗe shafin zuwa makon gobe domin ba ofishin mai ba da shawara na musamman kan tsare-tsare ƙarkashin jagorancin Hadiza Bala-Usman damar kammala aikin.

Yadda Tinubu zai rabu da wasu ministoci

A cewar Hadiza Bala-Usman, za a ɗauki matakin sauke ministocin da ba su yi aikin da ya kamata bane ta hanyar bin muhimman matakai guda uku.

Kara karanta wannan

Abin farin ciki yayin da Shugaba Tinubu ya yi sabbin naɗe-naɗe 2 masu muhimmanci a Ramadan

1. Matakin farko shi ne ra'yoyi da tantancewar ƴan Najeriya

2. Mataki na biyu kuma na hannun ofishin kula da tsare-tsare.

3. Na ƙarshe kuma shi ne wata tawagar masu bada shawari za su tantance ayyuka da ƙoƙarin kowane minista zuwa yanzu

"Saboda haka wadannan za su zama ginshikin tantance ko wane Minista da zai ci gaba da aiki da waɗanda za su bar cikin gwamnati saboda sun gaza,"

in ji Hadiza.

Tinubu ya yi sabbin naɗi a gwamnati

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya yi sababbin naɗe-naɗe domin gyara tawagar shugabannin hukumar almajirai da yaran da ba su zuwa makaranta

Shugaban ƙasar ya naɗa Birgediya Janar Lawal Ja'afar Isa (mai ritaya) a matsayin sabon shugaban majalisar da ke kula da hukumar almajirai

Asali: Legit.ng

Online view pixel