Ondo 2024: SSG Ta Ayyana Shirinta Na Tsaya Wa Takarar Gwamna

Ondo 2024: SSG Ta Ayyana Shirinta Na Tsaya Wa Takarar Gwamna

  • Princess Oladunni Odu, Sakatariyar gwamnan jihar Ondo ta ayyana burinta na neman takarar gwamna a zaben 2024
  • SSG ta bayyana cewa jihar Ondo na buƙatar mace a matsayin gwamna kuma a shirye take ta gaji gwamna Akeredolu na APC
  • Ta yi bayanin cewa ita ce kaɗai 'yan takara ɗaya tilo da ta cancanci zama gwamna a zaben shekara mai zuwa

Ondo state - Sakatariyar gwamnatin jihar Ondo, Princess Oladunni Odu, ta tabbatar da burinta na shiga tseren takarar gwamna a zaben jihar da ke tafe a shekara mai zuwa.

Princess Odu ta bayyana cewa ba abu ne mai wahala ba a samu mace a matsayin gwamnan jihar Ondo ba, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Sakatariyar gwamnatin jihar Ondo, Princess Odu.
Ondo 2024: SSG Ta Ayyana Shirinta Na Tsaya Wa Takarar Gwamna Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Sakatariyar gwamnatin (SSG) ta yi wannan furucin ne a Akure, babban birnin jihar yayin hira da mambobin ƙungiyar 'yan jarida ta ƙasa (NUJ) ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Sabon Rikici: Dakarun 'Yan Sanda Sun Mamaye Babbar Sakatariyar APC Ta Ƙasa, Bayanai Sun Fito

Ta ƙara da cewa a halin yanzu ita kaɗai ce 'yar takara ɗaya tilo da ke da kwarewar da ake buƙata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mata na da muhimmanci - Princess Odu

Odu, wadda ita ce mace ta farko da aka nada SSG a tarihin jihar, ta ce mata na da matukar muhimmanci a cikin al’umma, kuma fasahar jagoranci da halayensu za su kawo sauye-sauye da ci gaba.

Jaridar Daily Trust ta rahoto. SSG tana cewa:

“Ina da yakinin cewa samun mace ta farko a matsayin gwamna ba zai zama abu mai wahala ba. Ya dogara ne ga mutane da tunaninsu da yadda muke magana da mu'amala da su."
"Idan ku a matsayinku na 'yan jarida kun yi tafiya mai nisa kun ga abin da ke faruwa a wasu wuraren, za ku gaya wa mutane cewa lokaci ya yi da za mu sanya mace a matsayin gwamnan jiharmu."

Kara karanta wannan

Bayan Dogon Lokaci, Gwamnan PDP Ya Ƙara Wa Ma'aikata N10,000 a Albashi, Ya Rage Ranakun Zuwa Aiki

Odu ta kara da cewa babu wata mace da aka zaba a matsayin zababbiyar gwamna tun dawowar mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999 a Najeriya.

Ta ce ita ce ta fi cancantar kujerar gwamna kuma a shirye take ta karbi mulki daga hannun Gwamna Rotimi Akeredolu, wanda zai kammala wa’adinsa na biyu a karkashin jam’iyyar APC.

Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Manyan Malaman Musulunci

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu na gana wa yanzu haka da wakilan Malumman addinin Musulunci a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Wannan taro na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan tawagar Malamai sun gana da jagoran sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel