"Ba Zaku Iya Faɗa da Ni Ba" Shugaba Tinubu Ya Ɗau Zafi, Ya Aike da Saƙo Mai Ɗumi Ga NLC

"Ba Zaku Iya Faɗa da Ni Ba" Shugaba Tinubu Ya Ɗau Zafi, Ya Aike da Saƙo Mai Ɗumi Ga NLC

  • Bola Ahmed Tinubu ya caccaki kungiyar kwadago ta ƙasa NLC kan zanga-zangar da ta yi domin nuna adawa da tsadar rayuwa da yunwa
  • Shugaban ya ce ba zai yiwu NLC ta yaƙi gwamnatin da ba ta wuce wata 9 ba, yana mai cewa ba su ne kaɗai ke magana da muryar ƴan Najeriya ba
  • Tinubu ya aike da wannan sako ga NLC ne yayin da yake kaddamar da layin dogo a jihar Legas ranar Alhamis

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, a ranar Alhamis, 29 ga watan Fabrairu, ya yi Allah wadai da zanga-zangar da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta yi.

Shugaban ya gargaɗi ƴan kwadagon cewa ya kamata su sani ba su ne kaɗai muryar ƴan Najeriya ba, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya kai ziyara fadar fitaccen Sarki, ya yi magana mai jan hankali kan gwamnan da ya rasu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
"Ba Zaku Iya Fada Da Ni Ba" Shugaba Tinubu Ya Caccaki NLC kan Zanga-Zanga Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Tinubu ya yi wannan furucin ne a wurin kaddamar da layin dogo 'Red Line' wanda ya haɗa Agbado da Oyingbo a mahaifarsa watau jihar Legas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Talata ne kungiyar kwadago ta gudanar da zanga-zangar nuna adawa da tsadar rayuwar da ake ciki da rashin aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma wa.

Wane zazzafan martani Tinubu ya yi kan zanga-zanga?

Amma Tinubu ya ja kunnen NLC a yayin jawabinsa, inda ya ce ya kamata ta fahimci cewa duk da ‘yancin da take da shi, ba za ta iya yakar gwamnatin da ba ta wuce wata 9 ba.

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa babu gudu babu ja da baya dangane da sauye-sauyen da ya faro duk da turjiyar da yake fuskanta daga wadanda ya kira ‘yan fasa-kwauri.

A rahoton The Nation, Bola Tinubu ya ce:

Kara karanta wannan

"A ƙara haƙuri" Abu 1 da aka buƙaci Shugaba Tinubu ya yi domin magance tsadar rayuwa a Najeriya

"Ku bar ni na gudanar da aiki na, ya kamata ƴan kwadago su fahimci cewa ba su kaɗai ke da ƴanci da haƙƙi ba. Idan kuna son shiga zaɓe ne mu haɗu a 2027.
"Idan ba haka ba ku mana shiru a zauna lafiya, ba ku kaɗai bane kuke magana da muryar ƴan Najeriya."

Tinubu ne ya fara tunanin gina Red Line?

Shugaban ƙasar ya ce wannan layin dogo da ya kaddamar yana ɗaya daga cikin abubuwan da ya hango shekara 25 da suka wuce lokacin yana matsayin gwamnan Legas.

Ya kuma yi kira da a kara yauƙaƙa hadin gwiwa tsakanin ma’aikatar sufuri da sauran jihohi domin gina titunan jiragen kasa a fadin kasar nan.

Nawa ake siyar da litar fetur a ƙasashen duniya?

Rahoto ya zo cewa matsakaicin farashin man fetur a duniya shi ne Dalar Amurka 1.31 watau kwatankwacin Naira 2,000 kenan a kuɗin Najeriya kan kowace lita ɗaya.

Amma akan samu banbancin farashin man fetur a wasu ƙasashen. Legit Hausa ta tattaro muku farashin fetur a wasu ƙasashen Afirka a Naira da kuma dalar Amurka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel