Tsohon Hadimin Buhari Ya Nemi Gwamnatin Abba Tayi Koyi da Gwamnonin Jihar Legas

Tsohon Hadimin Buhari Ya Nemi Gwamnatin Abba Tayi Koyi da Gwamnonin Jihar Legas

  • Bashir Ahmaad zai so ganin gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta fara ganin yadda za a samar da jiragen kasa a garin Kano
  • Hadimin na Muhammadu Buhari bai da ra’ayin cinkoso yayi yawa, akwai bukatar a sake gina manyan gadoji na sama
  • Idan so samu ne, Malam Bashir Ahmaad yana so a samu layin dogo ya zagaye Rijiyar Lemu Mil Tara da ‘Yar Lemu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Bashir Ahmaad wanda ya shafe shekaru kusan bakwai a fadar shugaban kasa, ya ba gwamnatin NNPP shawara a Kano.

Malam Bashir Ahmaad yana so gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta fara shirin yadda za a samar da jirgin kasa a duk fadin jihar Kano.

Kara karanta wannan

Abin da Gwamna Abba ya fadawa malaman Kano da aka sa labule a fadar gwamnati

Abba Kano
Ana so Abba ya gina jirgin kasa a birnin Kano Hoto: @KYusufAbba @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Abba: Ina ma Kano ta zama kamar Legas

Hadimin tsohon shugaban Najeriyan yana ganin wannan zai taimaka ya rage saukin zirga-zirga, ya bunkasa kasuwanci da ilmi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bashir Ahmaad ya yi wadannan magangunu ne a dandalin X bayan ganin Bola Tinubu ya kaddamar da wani aikin dogo a Legas.

Kano za ta samu jirgin kasan cikin gari?

‘Dan siyasar ya yi wa al’ummar Kano sha’awar tsarin jirgin kasa a cikin gari wanda zai hada unguwar Na’ibawa zuwa ‘Yankaba.

A ganinsa zai yi kyau mutumin Rijiyar Zaki ya tafi Hotoro cikin sauki, a samu layin dogo tun daga Rijiyar Lemu zuwa Dawanau.

Tsohon ‘dan takaran kujerar majalisar tarayyar ya yi karin haske da cewa shawara yake ba Abba Yusuf ba sukar gwamnatinsa ba.

Wannan zai fi taimakawa al’umma a kan gina karin gadojin sama ko na tsallaka titi a birane kuma zai taimaki 'yan kasuwa sosai.

Kara karanta wannan

Abin da ya sa Bola Tinubu da APC suke tsoron Atiku a takarar Shugaban Kasa

"Wata rana layin dogo zai zagaye Legas. Ina yi masu murna sosai, kuma zan cigaba da kira a yi koyi da wannan a jihata, Kano."
"Ganin adadin al’umma a Kano, za a samu riba da aikin gina jirgin kasa."

- Bashir Ahmaad

Gwamnonin Kano su bi bayan Abba

Ba dole ba ne sai gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta kammala wannan aiki, tsohon ‘dan jaridar ya ce za a iya yin shekaru kafin a gama.

A jihar Legas, gwamnatocin Babatunde Fashola, Akinwumi Ambode da Babajide Sanwo Olu duk sun bi tafarkin Bola Tinubu ne.

Abba ya hadu da malaman Kano

Da zarar gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta saki layi, an ji labari cewa gwamna yana so malaman musulunci su maido shi kan hanya.

Mai girma gwamna yana so malaman addini su fada masa inda ya yi ba daidai ba domin ya gyara saboda a farfado da darajar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel