Jigon PDP Ya Tona Abin da Ya Jawo Wike Ya Goyi Bayan Tinubu a Kan Atiku a 2023

Jigon PDP Ya Tona Abin da Ya Jawo Wike Ya Goyi Bayan Tinubu a Kan Atiku a 2023

  • Mark Jacob ya taba rike mukami a majalisar NWC a PDP, ya yi maganar abubuwan da suka faru a zaben 2023
  • ‘Dan siyasar ya zargi Nyesom Wike da ‘yan kungiyar G5 da zama silar rashin nasarar Atiku Abubakar da PDP a bara
  • Jacob ya bada shawarar a dauki mataki a kan tsohon gwamnan Ribas saboda yadda ya taimaki APC da Bola Tinubu

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Tsohon mai bada shawara a kan harkokin shari’a a jam’iyyar PDP, Mark Jacob, ya dawo da maganar siyasar zaben 2023.

Da aka zanta da shi a tashar Arise a makon nan, Mark Jaco ya fadi abin da ya sa Nyesom Wike ya marawa takarar Bola Tinubu baya.

Kara karanta wannan

Muhimman matakai 6 da aka dauka da Tinubu ya zauna da Gwamnoni a Aso Villa

Tinubu Wike Atiku
Nyesom Wike ya bi Bola Tinubu a madadin Atiku a 2023 Hoto: Bola Ahmed Tinubu/Nyesom Ezenwo Wike/Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Nyesom Wike ya ci amanar PDP

Duk da yana gwamna kuma wanda ya nemi tikitin shugaban kasa, Wike bai goyi bayan takarar Atiku Abubakar a zaben 2023 ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon gwamnan na Ribas da irinsu Ifeanyi Ugwuanyi, Samuel Ortom, Okezie Ikpeazu da Seyi Makinde sun yi wa PDP zagon-kasa.

A karshe kuwa Bola Tinubu ya samu mulki, ya doke Atiku Abubakar da Peter Obi na LP, sai aka ba Wike kujerar Ministan birnin Abuja.

Meyasa Wike ya bi Tinubu a maimakon Atiku?

Marc Jacob ya ce Wike da sauran mutanensa wadanda ya kauracewa amaton sunayensu sun yaki PDP ne saboda tsabagen son rai.

Masanin shari’ar ya ce da gangan wadannan jagorori su ka ga bayan ‘dan takaransu kuma wannan ya jawowa PDP rashin nasara a 2023.

An so PDP ta fito da mutumin Kudu a 2023

Kara karanta wannan

"Ya dauki nauyin kawunnai na 10 zuwa Hajji": Tambuwal ya tuna haduwarsu ta karshe da Wigwe

Premium Times ta rahoto Jacob yana cewa Wike ya dage sai mulki ya koma kudu ne saboda yana da burin zama sabon shugaban Najeriya.

"Matsayata ita ce ba za ka taba yin nasara idan ka na yakar gidanka ba."
"Kowa ya san cewa maganar mulki ya koma wani yanki da Wike da mutanensa su ke yi son kai ne kurum."
"Ba saboda kowa ake fafutukar ba, domin idan haka ne, mutane irinsu Peter Obi ya kamata a ba tutan PDP."

- Mark Jacob

PDP ta gagara hukunta Wike da 'Yan G5

Jacob yana ganin ya kamata Wike ya yi murabus, ya fita daga jam’iyyar PDP, idan kuwa bai yi haka ba, ya ce kyau manya su ladabtar da shi.

Ministan da mutanensa sun zama ala-ka-kai, ba a kore su daga jam'iyyar PDP ba.

Wike a kujerar Ministan Abuja

An ji labari Nyesom Wike ya kara harajin makarantun boko. Gwamnati tace kudin neman gurbi a kowace makaranta ya koma N40, 000.

A sabon tsarin da aka kawo, ana karbar kudi ne gwargwadon kudin karantar da dalibai da kuma adadinsu a maimakon ayi kudin goro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel