Zaben 2023: Ina Goyon Bayan Matsayar Gwamnonin APC Na Mulki Ya Koma Kudu, Wike

Zaben 2023: Ina Goyon Bayan Matsayar Gwamnonin APC Na Mulki Ya Koma Kudu, Wike

  • Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya sake bi a kaikaice ya ayyana goyon baya ga Bola Ahmed Tinubu na APC
  • Yayin karkare kamfen PDP a kananan hukumomin Ribas, Wike ya ce yana goyon bayan matsayar gwamnonin APC
  • Gwamnan ya sanar da mutanen Ribas wanda zasu zaɓa a zaɓen shugaban kasa mai zuwa

Rivers - Gwamnan Ribas, Nyesom Wike, ya sake wayon nuna goyon bayansa ga ɗan takarar shugaban kasa a inuwar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a zaben 2023.

Rahoton Vanguard yace mako ɗaya gabanin zaɓen shugaban kasa, gwamma Wike ya bayyana cewa yana goyon bayan matsayar gwamnonin APC cewa mulki ya koma kudu.

Gwamna Wike.
Zaben 2023: Ina Goyon Bayan Matsayar Gwamnonin APC Na Mulki Ya Koma Kudu, Wike Hoto: Nyesom Wike
Asali: Facebook

Wike ya ƙara da cewa mutanen jihar Ribas ba su buƙatar sai an zo an faɗa masu wanda zasu zaba a matsayin shugaban kasa na gaba a Najeriya.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Kara Shiga Tasku, Gwamnan PDP Ya Yanke Shawara Ta Karshe Ya Faɗi Wanda Yake Goyon Baya a 2023

Gwamnan ya faɗi haka ne yayin jawabi ga magoya baya a wurin ralin kadammar da kamfen PDP na ƙarshe a kananan hukumomin Ribas wanda ya gudana a mahaifarsa Obio/Akpor ranar Asabar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jagoran G-5 ya ce:

"Zamu fita zaɓe domin haɗa kan Najeriya, zamu yi zaɓe domin adalci da daidaito. Shiyasa na jinjinawa gwamnonin APC, waɗanda suka ce idan ana son haɗin kai, a tafi tare, wajibi a yi mulkin karba-karba."
"Sun san Najeriya kasa ce dake bukatar zama a dunƙule, masu son kai da habo-habon neman mulki, ba su gane cewa zaka iya samun mulki amma ka rasa zaman lafiya ba."
"Zai fi kyau ka samu zaman lafiya da natsuwa ta yadda idan ka samu mulki ka iya shugabantar mutane yadda ya kamata."

The Nation ta ce da yake sukar ɗan takarar shugaban kasa na PDP a kaikaice kan raina karfin kuri'un jihar Ribas, gwamna Wike ya ci gaba da cewa:

Kara karanta wannan

Bayan Wike, Bola Tinubu Ya Lallaɓa Wurin Wani Gwamnan PDP Ana Dab da Zaɓen 2023

"Duk wanda ba ya sha'awar jiharmu, ba zamu zaɓe shi ba saboda haka baku buƙatar sai wani ya zo ya faɗa maku wanda zaku jefa wa kuri'unku."

Atiku ya ƙara samun gagarumin goyon baya

A wani labarin kuma Jam'iyyun Siyasa 5 Sun Rushe Tsarinsu, Sun Koma Bayan Atiku a zaben 2023

Wasu jam'iyyun siyasa guda a biyar sun janye daga takara, sun ayyana cikakken goyon baya ga mai neman zama shugaban kasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar.

Sun sanar da haka ne a wurin ralin karshe na kamfen jam'iyyar PDP wanda ya gudana yau Asabar a jihar Adamawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel