“Ya Dauki Nauyin Kawunnai Na 10 Zuwa Hajji”: Tambuwal Ya Tuna Haduwarsu Ta Karshe da Wigwe

“Ya Dauki Nauyin Kawunnai Na 10 Zuwa Hajji”: Tambuwal Ya Tuna Haduwarsu Ta Karshe da Wigwe

  • Jama'a na ci gaba da yin martani kan mutuwar shugaban bankin Access, Herbert Wigwe wanda ya mutu a hatsarin jirgi mai saukar ungulu a Amurka
  • Sanatan PDP, Aminu Tambuwal ya shiga jerin masu alhinin mutuwar biloniyan wanda ya bayyana a matsayin aboki
  • Tambuwal ya fashe da kuka a majalisar dayyawa yayin da yake tuna haduwarsu ta karshe da attajirin, cewa ya so ya duba sabon jami'ar da ya gina amma Allah bai nufa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Abuja - Sanata mai wakiltar Sokoto ta Kudu, Aminu Tambuwal, ya yi martani akan mutuwar Herbert Wigwe, tsohon shugaban kamfanin Access Holdings Group.

A ranar Laraba, 14 ga watan Fabrairu, Tambuwal, ya tuna haduwarsu ta karshe da marigayi shugaban bankin na Access yayin da yake jawabi a zaman majalisar dattawa.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP sun aikawa Bola Tinubu sako kan mugun hadarin da ake fuskanta

Tambuwal ya yi alhinin rashin Wigwe
“Ya Biyawa Kawunnai Na 10 Hajji”: Tambuwal Ya Tuna Haduwarsu Ta Karshe da Wigwe Hoto: Aminu Waziri Tambuwal, @HerbertOWigwe
Asali: Twitter

Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, sanatan na PDP ya bayyana cewa Wigwe ya so ace ya duba aikin gina jami'ar sa, "amma, wannan ranar ba zai taba zuwa."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ku tuna cewa Wigwe, matarsa, Doreen, dansa da tsohon shugaban kungiyar chanji na Najeriya, Abimbola Ogunbanjo; da sauransu a hatsarin jirgi mai saukar ungulu a Amurka a ranar Juma'a.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da masu binciken Amurka suka ce za a kai tarkacen jirgin da ya yi hadari zuwa wani sabon wuri a Amurka domin yin gwaje-gwaje masu inganci a ranar Talata, 13 ga watan Fabrairu.

Maganar karshe da muka yi da Wigwe, Tambuwal ya magantu

Da yake magana a zauren majalisar dattawa a ranar Laraba, Tambuwal ya ce:

"Yayin da nake matsayin gwamnan jihata, ya ziyarce ni. Ya tambayi kawunnai na abin da zai yi masu. Sun roke shi da ya kai su hajji. Ya basu kujeru 10 a matsayinsa na Kirista don su je hajji. Haka Herbert Wigwe yake.

Kara karanta wannan

"Rayuwa babbar kyauta ce": Sakon karshe da shugaban bankin Access ya saki kafin hatsarin jirgi

"Mun yi magana ta karshe a ranar 1 ga watan Fabrairu. Ya ce ya kira ne don ya gaishe ni saboda mun dade ba mu ga juna ba. Ya so na kai masa ziyara sannan na duba aikin jami'ar Wigwe. Toh dai, wannan rana ba zai taba zuwa ba kuma."

Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan asusun gwamnati, Sanata Ahmed Wadada, ya bayyana Wigwe a matsayin mutum da ke zuwa "ko'ina yana yin duk abin da zai iya kawo ci gaba ga al'umma."

Sai dai kuma, majalisar dattawan ta yi kira ga gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu da ta baiwa hukumomin Amurka hadin kai domin ganin an gudanar da cikakken bincike, rahoton Nigerian Tribune.

An gano sakon Wigwe na karshe

A wani labarin, Herbert Wigwe, marigayi shugaban bankin Access, ya kasance mai karafafa gwiwa ga 'yan Najeriya, har lokacin da yake gab da barin duniya.

A shafukansa na soshiyal midiya, marigayin yana yawan sanar da mabiyansa ayyukansa sannan ya kan karfafa masu gwiwa da yi masu zantuka masu dadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel