Dan Takarar Gwamna a APC Ya Janye Bayan Mutuwar Dansa Kwana Kadan Kafin Zabe, Ya Roki Jama’a

Dan Takarar Gwamna a APC Ya Janye Bayan Mutuwar Dansa Kwana Kadan Kafin Zabe, Ya Roki Jama’a

  • Tsohon dan Majalisar Tarayya ya janye takarar gwamnan da ya ke nema a jihar Edo saboda mutuwar dansa
  • Ehiozuwa ya na takarar gwamnan ne a jam’iyyar APC a jihar a zaben da za a gudanar a karshen wannan shekara
  • Dan Ehiozuwa mai suna Osazuwa Michael ya rasu ya na da shekaru 23 a duniya a jihar Texas da ke Amurka

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo – Dan takarar gwamna a jihar Edo, Ehiozuwa Agbonayinma ya janye takararsa saboda mutuwar dansa a kwanakin baya.

Ehiozuwa wanda tsohon mamban Majalisar Tarayya ne ya na takara a jam’iyyar APC a jihar a zaben da za a gudanar a karshen wannan shekara.

Kara karanta wannan

A karshe, Tinubu ya janye tuhumar da ake kan dan takarar shugaban kasa da Buhari ya gurfanar

Dan takarar gwamnan APC ya janye saboda mutuwar dansa
Dan Takarar Gwamna a APC a jihar Edo Ya Janye Takara Bayan Mutuwar Dansa. Hoto: Ehiozuwa Agbonayinma, Osazuwa Michael.
Asali: Facebook

Mene dan takarar ke cewa?

Dan Ehiozuwa mai suna Osazuwa Michael ya rasu ya na da shekaru 23 a duniya a Texas da ke Amurka, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan takarar shi ne ya fara sanar da shugabancin jam’iyyar cewa zai tsaya takara a zaben da za a gudanar, cewar EkoHotBlog.

Yayin da ya ke jawabi ga magoya bayansa, Ehiozuwa ya bukace su da su goyi bayan duk wanda ya yi nasara a zaben fidda gwani.

Za a gudanar da zaben fidda gwanin ne a ranar Asabar mai zuwa 16 ga watan Faburairu a jihar.

Rokon da dan takarar ya yi

A cewarsa:

“Fiye da shekara ina tunanin tsayawa takara bayan kiraye-kirayen jama’a daga jihar da kasashen ketare.
“Na fara tuntubar mutane da dama da suka hada da ‘yan siyasa da sarakunan gargajiya inda na samu tarba da kuma goyon baya sosai.

Kara karanta wannan

NNPP ta yadu zuwa wajen Kano, Jam’iyya Ta Samu ‘Dan Majalisa a Jihar Nasarawa

“Sai dai kuma iyalai na sun hadu da babbar jarabawa bayan rasuwar danmu mai suna Osazuwa bayan an harbe shi a Amurka.”

Ehiozuwa ya ce bai dade da dawowa daga Amurka ba bayan an binne shi inda ya ce wannan babban masifa ce wanda babu wanda zai so hakan ya faru da shi, cewar Leadership.

Ya kara da cewa:

“A yanzu ina cikin alhini kuma bani da karfin tsayawa takara a halin da nake ciki, bayan tuntubar jama’a na yanke shawarar dakatar da tsayawa takara.
“Ina mika godiya ga al’umma da irin gudunmawar da suka nuna min ta ko wane bangare.”

Dan tsohon mamban Majalisa ya mutu

Kun ji cewa wani matashi mai suna Osazuwa Agbonayinma ya rasa ransa a Amurka bayan an harbe shi.

Marigayin wanda dan shekaru 23 ne ya kasance dan tsohon dan Majalisar Tarayya, Ehiozuwa Agbonayinma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel