INEC Ta Ayyana Zaben Majalisar Tarayya a Matsayin Wanda Bai Kammala Ba a Jihar Arewa, Akwai Dalili
- Yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaben cike gurbi, hukumar INEC ta ayyana zaben a Taraba wanda bai kammala ba
- Hukumar ta bayyana cewa zaben mazabar Jalingo/Yorro/Zing a Majalisar Tarayya bai kammala ba a yau Lahadi
- An gudanar da zaben ne tsakanin dan takarar jam'iyar PDP, Sadiq Tafida da kuma na jam'iyyar SDP, Innocent Jabayang
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Taraba - Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta ayyana zaben Majalisar Wakilai a jihar Taraba wanda bai kammala ba.
Hukumar ta bayyana haka ne bayan kammala zabe a mazabar Jalingo/Yorro/Zing a jihar, cewar Vanguard.
Wane mataki hukumar INEC ta dauka?
An gudanar da zaben ne tsakanin dan takarar jam'iyar PDP, Sadiq Tafida da kuma na jam'iyyar SDP, Innocent Jabayang.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tafida ya samu kuri'u dubu 17,214 yayin da dan jam'iyyar SDP, Innocent ya samu kuri'u dubu 15,537.
Baturen zaben, Farfesa Daniel Ayuba ya ce ratar kuri'un bai wuce 1,677 yayin da aka soke kuri'u dubu 14,759, cewar Channels TV.
Ayuba ya ce matakin ya zama dole ganin yadda ratar da ke tsakanin 'yan takarar bai kai yawan kuri'un da aka soke ba.
Martanin Kungiyar CAN a Taraba
Wannan na zuwa ne bayan Kungiyar Kiristoci, CAN a jihar Taraba ta karyata jita-jitar tilasta dan takara janyewa.
Kungiyar ta ce ba ta san da maganar ba wacce ake yadawa cewa ta tilasta dan takarar SDP, Innocent Jabayang janyewa ga dan PDP, Sadiq Tafida.
Kungiyar ta ce ta samu labarin ne bayan dan takarar ya yi zama da Gwamna Agbu Kefas inda gwamnan ya nemi ya janyewa dan PDP.
INEC ta sanar da sakamakon zaben Kano
Kun ji cewa hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta sanar da sakamakon zaben cike gurbi a jihar Kano.
Hukumar ta ayyana Bello Muhaammad Butu-Butu a matsayin wanda ya yi nasara a zaben mazabar Rimin Gado/Tofa.
Wannan na zuwa ne bayan hukumar INEC ta soke zaben mazabar Kunchi/Tsanyawa bayan samun rikici a wuraren.
Asali: Legit.ng