CAN Ta Tilasta Dan Takara Janyewa Dan Jam’iyyar PDP a Zaben Cike Gurbin Taraba? Gaskiya Ta Fito

CAN Ta Tilasta Dan Takara Janyewa Dan Jam’iyyar PDP a Zaben Cike Gurbin Taraba? Gaskiya Ta Fito

  • Kungiyar CAN a jihar Taraba ta yi fatali da jita-jitar cewa ta tilasta dan takarar SDP janyewa na jam’iyyar PDP
  • Shugaban kungiyar a jihar, Rabaran Magaji Jirapye shi ya bayyana a yau Asabar 3 ga watan Faburairu a Jalingo
  • Kungiyar ta ce dan takarar ya janye ne bayan Gwamna Kefas ya tuntube shi kan bai wa jam’iyyar PDP dama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Taraba – Kungiyar CAN reshen jihar Taraba ta yi martani kan jita-jitar dakatar da dan takarar jam’iyyar SDP.

Kungiyar ta ce wannan labarin ba shi da tushe bare makama inda ta ce ita ma samun labarin ta ke daga baya.

Kara karanta wannan

An shiga rudani a Jos bayan Hukumar INEC ta cire sunan PDP a zaben cike gurbi, APC da LP sun shiga

Kungiyar CAN ta yi martani kan zargin tilasta dan takara janyewa PDP
CAN ta karyata jita-jitar tilasta dan takara janyewa PDP. Hoto: Agbu Kefas.
Asali: Twitter

Mene martanin kungiyar CAN?

An ruwaito cewa kungiyar ta shawarci dan takarar SDP, Innocent Jabayang ya janyewa dan takarar PDP, Sadik Tafida a zaben cike gurbi da ake gudanarwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kungiyar a jihar, Rabaran Magaji Jirapye shi ya bayyana a yau Asabar 3 ga watan Faburairu a Jalingo, cewar Tribune.

Idan ba a mantaba ana zaben cike gurbin ne don samun madadin mamban da ke wakiltar mazabar Jalingo/Yorro/ Zing a mazabar Tarayya.

Wannan ya biyo bayan rasuwar Isma’ila Maihanchi wanda ya yi nasara a zaben da aka gudanar a watan Faburairun 2023.

Jirape ya ce Jabayang ya janye da kansa bayan Gwamna Kefas ya tuntube shi don bai wa jam’iyyar PDP dama.

Fitowar jama'a a zaben cike gurbin

Ya ce:

“Kungiyar CAN kawai ta samu labarin janyewar ne bayan an yanke hukunci saboda tun farko ta nuna goyon bayanta ga dan takarar SDP.

Kara karanta wannan

Watanni kadan bayan mutuwar shugabar matan PDP, an maye gurbinta da Amina, bayanai sun fito

"Lokacin da ya yanke hukuncin goyon bayan dan PDP, Gwamnan ya tuntube mu saboda matsayar mu a baya.
“Mun yi ganawa da dan takarar SDP inda ya tabbatar mana da matakin da ya dauka, CAN ba ta tilasta masa janyewa ba.”

Kokarin jin ta bakin Hon. Jayabang da 'yan jaridu suka yi ya ci tura bayan kira da kuma tura masa sakwannin kar-ta-kwana.

Leadership ta tabbatar da cewa an samu rashin fitowa zaben cike gurbin a wurare da dama a birnin Jalingo.

An soke zaben Kunchi a Kano

Kin ji cewa hukumar INEC ta soke wasu zabukan cike gurbi a jihohin Kano da Enugu da kuma Akwa Ibom.

Wannan na zuwa ne bayan samun tashe-tashen hankula a wasu rumfunan zabe da ake yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel