Dan Majalisa Ya Fashe da Kuka Ana Cikin Zaman Majalisa, An Fadi Dalili

Dan Majalisa Ya Fashe da Kuka Ana Cikin Zaman Majalisa, An Fadi Dalili

  • Mai magana da yawun majalisar wakilai ta Najeriya ya fashe da kuka ana tsaka da zaman majalisa
  • Akin Rotimi ya fashe da kuka ne yayin da yake magana kan matsalar rashin tsaro da ta addabi jiharsa ta Ekiti
  • Ɗan majalisar wanda ya koka kan kisan wasu sarakuna biyu da aka yi, ya buƙaci da a kai musu agaji ta hanyar tura jami'an tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Wani ɗan majalisar wakilan Najeriya ya fashe da kuka a ranar Talata a zauren majalisar yayin da yake magana kan matsalar rashin tsaro a jiharsa.

Duk da yake matsalar tsaro ta ƙara ta’azzara a fadin ƙasar nan, inda kusan kullum ake samun rahotannin kashe-kashe da garkuwa da mutane, ɗan majalisar ya mayar da hankali ne kan sabon lamarin da ya faru a jiharsa.

Kara karanta wannan

"Idan ba za ka iya ba ka sauka": Atiku ya caccaki Tinubu kan abu 1 tak

Dan majalisa ya fashe da kuka a zauren majalisa
Akin Rotimi ya damu da matsalar rashin tsaro.a.jihar Ekiti Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

A zauren majalisar wakilai, Akin Rotimi, mai magana da yawun majalisar, ya fashe da kuka a lokacin da yake karanta ƙudiri kan kashe wasu sarakuna biyu a jihar Ekiti ranar Litinin, cewar rahoton Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa ɗann majalisar yin kuka?

Mista Rotimi, wanda ke wakiltar mazaɓar Oye/Ikole, ya kasa danne zuciyarsa a lokacin da yake karanta ƙudirin.

A cikin ƙudirin nasa, ya yi kira da a kawo ɗauki na jami’an tsaro domin daƙile ta’addancin da ke addabar jihar Ekiti.

Ya ce an samu ƙaruwar aikata miyagun laifuka a mazabar tarayya ta Ekiti ta Arewa 1 (Ikole/Oye) a ƴan kwanakin nan wanda ke haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.

Mista Rotimi ya sanar da abokan aikinsa cewa wasu da ba a san ko su waye ba ne suka kashe sarakunan biyu.

Kara karanta wannan

"Ina cikin damuwa" Gwamnan PDP ya faɗi halin da yake ciki saboda rikicin siyasar jiharsa

Yayin da yake magana game da sarakunan, Mista Rotimi ya yi kuka da ƙarfi, inda wasu ƴan majalisar suka riƙa ba shi haƙuri ta hanyar shafa masa baya.

Daga ƙarshe majalisar ta yanke shawarar yin kira ga babban hafsan sojin ƙasar nan da ya tura sojoji yankin Oke-Ako don inganta tsaro da daƙile sake aukuwar waɗannan munanan ayyuka.

Atiku Ya Caccaki Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya caccaki Tinubu kan matsalar rashin tsaro.

Atiku ya buƙaci shugaban ƙasar da ya sauka daga muƙaminsa idan ba zai iya shawo kan matsalar rashin tsaron da ta addabi ƙasar nan ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel