Shugaba Tinubu Ya Fusata Kan Kisan da Aka Yi Wa Sarakunan Gargajiya, Ya Bayar da Sabon Umarni

Shugaba Tinubu Ya Fusata Kan Kisan da Aka Yi Wa Sarakunan Gargajiya, Ya Bayar da Sabon Umarni

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah wadai da kisan da aka yi wa wasu sarakunan gargajiya biyu a jihar Ekiti
  • Shugaban ƙasar ya kuma bayar da umarnin a gaggauta ceto ɗaliban makaranta da malamansu da aka sace a jihar
  • Tinubu a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa ya fitar, ya ba da tabbacin cewa za a hukunta miyagun da suka aikata wannan ta'asar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya nuna alhininsa kan kisan da aka yi wa wasu sarakunan gargajiya biyu a jihar Ekiti.

Shugaban ƙasar ya kuma bayar da umarnin a gaggauta ceto yara da malaman makaranta da aka yi garkuwa da su a kewayen yankin Eporo-Ekiti na jihar Ekiti.

Kara karanta wannan

"Idan ba za ka iya ba ka sauka": Atiku ya caccaki Tinubu kan abu 1 tak

Tinubu ya umarci a ceto daliban da aka sace a Ekiti
Shugaba Tinubu ya yi Allah wadai da kisan da aka yi wa sarakunan gargajiya a Ekiti Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Talata, 30 ga watan Janairun 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Tinubu yayi Allah wadai da wannan rashin tunani da zubar da jini, ya kuma yi alƙawarin cewa waɗanda suka aikata laifin ba za su kuɓuta daga fuskantar shari’a ba.

Tinubu ya yi ta'aziyyar sarakunan da aka kashe a Ekiti

Shugaban ƙasan ya jajantawa iyalai da talakawan sarakunan gargajiyan, Gwamna Biodun Oyebanji, da al’ummar jihar Ekiti kan wannan lamari mai matuƙar tayar da hankali.

Shugaban ƙasar ya kuma bayar da tabbacin cewa ana yi wa hukumomin tsaron ƙasar nan garambawul domin samar da sakamako mai kyau.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Cikin baƙin ciki Shugaba Bola Tinubu ya samu labarin kashe wasu sarakunan gargajiya biyu a jihar Ekiti, Onimojo na Imojo-Ekiti, Oba Olatunde Samuel Olusola, da Elesun na Esun-Ekiti, Oba David Babatunde Ogunsola.

Kara karanta wannan

"Ina cikin damuwa" Gwamnan PDP ya faɗi halin da yake ciki saboda rikicin siyasar jiharsa

"Shugaba Tinubu ya yi Allah-wadai da wannan rashin tunani da zubar da jini, ya kuma yi alkawarin cewa masu aikata laifin ba za su kuɓuta daga fuskantar shari'a ba.
"Shugaban ya jajantawa iyalai da talakawan sarakunan gargajiyan, Gwamna Biodun Oyebanji, da al’ummar jihar Ekiti kan wannan lamari mai matukar tayar da hankali."

Ɗan Majalisa Ya Fashe da Kuka a Zauren Majalisa

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani ɗan majalisar wakilai ta Najeriya, ya fashe da kuka ana tsaka da zaman majalisar.

Akin Rotimi ya fashe da kuka ne kan kisan da aka yi wa wasu sarakunan gargajiya a jiharsa ta Ekiti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel