Littafin Femi Adesina Ya Fallasa Asirin Fastoci a Lokacin da Buhari Yake Karagar Mulki

Littafin Femi Adesina Ya Fallasa Asirin Fastoci a Lokacin da Buhari Yake Karagar Mulki

  • Femi Adesina ya yi kaca-kaca da wasu fastoci a littafin da ya rubuta a game da mulkin Muhammadu Buhari
  • Marubucin yace wasu limaman coci sun yi wa APC adawa har aka koma yi wa gwamnatin kasar fatan sharri
  • Adesina ya ce karshe gwamnatin Muhammadu Buhari ta kunyata malaman karyan da ke ci da sunan addini

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Littafin Femi Adesina ya kawo labarin yadda fastoci suka dage da addu’o’i domin ganin Muhammadu Buhari bai ci zaben 2015 ba.

Daga nan kuma malaman addinin kiristan suka rika yi wa Muhammadu Buhari fatan rashin nasara, za a samu labarin nan a Vanguard.

Buhari
Femi Adesina da Muhammadu Buhari Hoto: Femi Adesina, Yemi Osinbajo
Asali: Twitter

Tun da Muhammadu Buhari ya sanar da duniya zai yi takara, Femi Adesina ya ce wasu fastoci suke masa adawa, suna goyon bayan PDP.

Kara karanta wannan

An kama wani matashi da ya kware wurin satar kayan coci, za a gurfanar da shi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adawar fastoci ga Buhari da APC

Marubucin ya ce Goodluck Jonathan ya rika ziyartar coci bayan coci domin ya zarce.

Adesina ya ce akwai wani Fasto Emanuel da ya fito da huduba inda ya yi kaca-kaca da APC da ‘dan takaranta, ya kira su da masu yin jihadi.

Wasu malaman addini sun yi fito na fito da gwamnatin Buhari, akwai faston da ya yi umarni a kashe duk Fulanin da ya zo kusa da cocinsa.

Fastoci sun ce Buhari zai fadi zabe

A cewar Adesina, da aka tambayi Fasto Enoch Adejare Adeboye game da zaben 2015, sai ya ce Ubangiji ya fada masa Jonathan zai yi nasara.

Da aka dawo zaben tazarce a 2019, hadimin shugaban kasar ya ce an sake samun malaman addini da suka ce Buhari ba zai koma ofis ba.

Kara karanta wannan

Na kusa da shi ya bayyana halin tausayi da Buhari ya shiga lokacin rashin lafiya

A zaben 2019, marubucin ya ce mai gidansa ya hada Atiku Abubakar da wannan fasto ya doke. Punch ta kawo labarin littafin na Adesina.

Adawar wasu Fastoci ga Buhari

A tsakiyar 2022, sai aka ji faston nan yana sukar gwamnatin Buhari da cewa ba a taba yin mulkin zalunci da rashin gaskiya kamar ta ba.

Limamin cocin ya kuma umarci mabiyansa da yin azumin kwanaki bakwai domin kawo karshen Buhari, wasu fastoci biyu suka biye masa.

...Adesina ya ce akwai Fastocin kwarai

A littafinsa mai shafi 488, Adesina ya ce saboda yadda fastonsa a Asokoro, Babajide Olowodola yake sukar Buhari, ya daina zuwa cocinsa.

Littafin ya yabi limaman coci irinsu Chris Okotie da Williamson Folorunsho Kumuyi wanda yace sun yi wa tsohon shugaban kasar adalci.

Rashin lafiyar Buhari

Ana da labari Mista Femi Adesina ya ce akwai lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari bai san inda yake ba da ciwo ya yi masa zafi.

Shugaban Najeriyan ya yi ta rashin lafiya da yake mulki har aka kai shi asibitin kasar waje, Adesina ya kawo labarin jinyar da Buhari ya yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel