Zaben 2019: Yadda ta kaya tsakanin shugaban kasa Buhari da Atiku
Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta tabbatar da nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayi dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar APC da ya lashe babban zabe da aka gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairun 2019.
Farfesa Mahmood Yakubu, babban Baturen zabe kuma shugaban hukumar zabe ta kasa wato INEC, ya tabbatar da nasarar shugaban kasa Buhari a matsayin zakara wanda ya lashe zaben da gamayyar kuri'u 15,191,847.
Cikin jawaban sa da misalin karfe 3.00 na daren yau Laraba bayan kammala kididdiga da kidayar dukkanin kuri'u daga jihohin 36 da ke fadin kasar nan, Farfesa Yakubu ya ce Buhari ya galaba akan babban abokin adawar sa, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar.
KARANTA KUMA: Sakamakon zabe daga jihohin Kano, Adamawa, Yobe da Borno
Kamar yadda fashin baki na adadin kuri'u suka zayyana cikin jihohin Najeriya, Farfesa Yakubu ya ce, Atiku bai yi nasaba yayin da ya tsira da kuri'u 11,262,978 kacal.
Jaridar Legit.ng ta kawo muku dalla-dalla yadda ta kaya tsakanin manyan 'yan takarar biyu cikin dukkanin jihohi 36 da ke fadin kasar nan da kuma garin Abuja kamar haka.
Jihar Abia
Atiku: 219,698
Buhari: 85,058
Jihar Adamawa
Atiku: 410,266
Buhari: 378,078
Jihar Akwa Ibom
Atiku: 395,832
Buhari: 175,429
Jihar Anambra
Atiku: 524,738
Buhari: 33,298
Jihar Bauchi
Buhari: 798,428
Atiku: 209,313
Jihar Bayelsa
Atiku: 197,933
Buhari: 118,821
Jihar Benuwe
Atiku: 356,817
Buhari: 347,668
Jihar Borno
Buhari: 836,496
Atiku: 71,788
Jihar Cross River
Atiku: 295,737
Buhari: 117,302
Jihar Delta
Atiku: 594,068
Buhari: 221,292
Jihar Ebonyi
Atiku: 258,573
Buhari: 90,726
Jihar Edo
Atiku: 275,691
Buhari: 267,842
Jihar Ekiti
Buhari: 219,231
Atiku: 154,032
Jihar Enugu
Atiku: 355,553
Buhari: 54,423
Jihar Gombe
Buhari: 402,961
Atiku: 138,484
Jihar Imo
Atiku: 334,923
Buhari: 140,463
Jihar Jigawa:
Buhari: 794,738
Atiku: 289,895
Jihar Kaduna
Buhari: 993,445
Atiku: 649,612
Jihar Katsina
Buhari: 1,232,133
Atiku: 308,056
Jihar Kano
Buhari: 1,464,768
Atiku: 391,593
Jihar Kebbi
Buhari: 581,552
Atiku: 154,282
Jihar Kogi
Buhari: 285,894
Atiku: 218,207
Jihar Kwara
Buhari: 308,984
Atiku: 138,184
Jihar Legas
Buhari: 580,825
Atiku: 448,015
Jihar Nasarawa
Buhari: 289,903
Atiku: 283,847
Jihar Neja
Buhari: 612,371
Atiku: 218,052
Jihar Ogun
Buhari: 281,762
Atiku: 194,655
Jihar Ondo
Atiku: 275,901
Buhari: 241,769
Jihar Osun
Buhari: 347,634
Atiku: 337,377
Jihar Oyo
Atiku: 366,690
Buhari: 365,229
Jihar Filato
Atiku: 584,665
Buhari: 468,555
Jihar Ribas
Atiku: 473,971
Buhari: 150,710
Jihar Sakkwato
Buhari: 490,333
Atiku: 361,604
Jihar Taraba
Atiku: 347,743
Buhari: 324,906
Jihar Yobe
Buhari: 497,914
Atiku: 50,763
Jihar Zamfara
Buhari: 438,682
Atiku: 125,423
Birnin Tarayya Abuja
Atiku: 259,997
Buhari: 152,224
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng