Buhari ga Kumuyi: Ziyararka ta karfafa mun guiwa

Buhari ga Kumuyi: Ziyararka ta karfafa mun guiwa

- Buhari ya karbi bakuncin babban Sufurtanda na cocin Deeper Life Bible, Pastor William Folorunso Kumuyi

- Ya ce ziyarar ta karfafa masa guiwa

- Buhari ya ce Allah bai yi kuskure ba, na kirkiri kabilu 250 tare da sanyasu a waje daya don zama a matsayin 'yan kasar Nigeria

A ranar litinin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin babban Sufurtanda na cocin Deeper Life Bible, Pastor William Folorunso Kumuyi, a fadar shugaban kasa da ke Abuja, inda shugaban kasar ya bayyana cewa ziyarar Kumuyi ta karfafa masa guiwa.

Shugaban kasa Buhari ya ce: "Ziyararka ta karfafa mun guiwa. Na gode matuka da wannan ziyara."

Shugaban kasar ya kuma ce hakika Allah bai yi kuskure ba, a lokacin da ya kirkiri kabilu 250 tare da sanyasu a waje daya don zama a wata kasa da ake kira Nigeria, yana mai jaddada muhimmanci na 'yan Nigeria su kasance masu godiya ga Allah da ya hada kan kowa a waje daya.

KARANTA WANNAN: Atiku Abubakar: Na tsamo iyalai 45,000 daga kangin talauci a Nigeria

Buhari ga Kumuyi: Ziyararka ta karfafa mun guiwa
Buhari ga Kumuyi: Ziyararka ta karfafa mun guiwa
Asali: Facebook

Da yake bayyana Nigeria a matsayin kasa mai alfarma, mai cike da mutane da albarkatun kasa, Buhari ya ce: "Muna fuskantar kalubale a kokarin mu na ganin jama'a sun fahimci hakan. A matsayina na wanda ya rike mukamin ministan man fetur, gwamna, shugaban kasa a mulkin soja, shugaban gidauniyar man fetur ta PTF, ina ganin kamar komai a bayyane ya ke a wajena."

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tuna wasu kyawawan ayyukan da Pastor Kumuyi ya gudanar a matsayinsa na malamin addini kuma malami a jami'a kafin komawarsa kacokan ga harkokin addini.

Buhari ga Kumuyi: Ziyararka ta karfafa mun guiwa
Buhari ga Kumuyi: Ziyararka ta karfafa mun guiwa
Asali: Facebook

Ya jinjinawa malamin majami'ar da ya amsa gayyatar gwamnati na gabatar da wa'azi a bukin cikar Nigeria shekaru 58 da samun 'yanci daga mulkin turawan mallaka, kana ya gode masa da wannan ziyara.

A yayinn ziyarar, babban Sufurtandan ya samu rakiyar matarsa, Esther, da kuma Pastor Samuel Afuwape, Pastor Chike Onwuasoanya tare da Pastor Seyin Malomo.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng