Jonathan ya nemi shugaba Buhari ya yi koyi da nagarta ta Magabatan kwarai na PDP

Jonathan ya nemi shugaba Buhari ya yi koyi da nagarta ta Magabatan kwarai na PDP

Tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan, a jiya Juma'a ya mayar da martani ga fadar shugaban kasa da kuma gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, dangane da caccakarsa kan ababen da sabon littafin da ya wallafa ya kunsa.

Jonathan cikin sabon littafinsa da ya kaddamar can garin Abuja a ranar Talatar da ta gabata, ya bayyana yadda sakacin gwamnan jihar Borno ya yi sanadiyar yashe 'yan Matan Chibok a shekarar 2014 tare da ikirarin yadda gwamnatin shugaba Buhari ta gaza wajen yakar rashawa.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa kwazon gwamnatinsa wajen yakar rashawa ta yi wa ta gwamnatin shugaba Buhari fintinkau ta kowace siga mai tasirin gaske.

Sabon littafin na tsohon shugaban kasa ya janyo harzuka gami da fushin gwamnan jihar Borno inda a cewarsa ya bayyana wallafarsa a matsayin tatsuniyoyi da labarai na shaci fadi.

Kazalika fadar shugaban kasa yayin mayar da martanin ta da sanadin kakakin shugaban kasa Mallam Garba Shehu, ta bayyana cewa tasirin yaki da rashawa na gwamnatin tsohon shugaban kasa bai ko iya hada sahu ko gogayyar kafada da na gwamnatin Buhari.

Buhari ya yi koyi da Tarihin nasarorin PDP - Jonathan
Buhari ya yi koyi da Tarihin nasarorin PDP - Jonathan
Asali: Twitter

Mallam Shehu ya bayyana cewa, wallafar wannan lamari na rashawa cikin sabon littafin tsohon shugaban kasa ba ya da wasu dalilai ko hujjoji da za su tabbatar da ikiraransa illa iyaka tsagwaran adawa da gwamnatin shugaba Buhari.

Tsohon shugaban kasar cikin wata sanarwa da sanadin hadiminsa mai kiciniyar hulda da manema labarai, Ikechukwu Eze a ranar Juma'ar da ta gabata ya bayyana cewa, ma su caccakar sabon littafin ba bu abinda suka nufata face kawo nakasu da raunana aminci da kuma sahihancinsa.

KARANTA KUMA: Gwamnatin Tarayya ta shirya fatattakar ta'ammali da fataucin miyagun kwayoyi

Ya kara da cewa, a madadin ci gaba da damuwa tare da adawa da sahihancin wannan littafi, Eze ya nemi gwamnatin shugaba Buhari ta yi riko tare da lizimtar tarihin nasarori da gwamnatin PDP ta magabatan kwarai ta samu a kasar nan.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, kungiyar dattawan Arewa ta bayyana yadda rashin cika alkawari da kuma rashin mutunta yarjejeniya ta sanya yankin Arewa ya yi adawa tare da juya baya ga tsohon shugaban kasa Jonathan a zaben 2011 da kuma na 2015.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel