Bayan Karkare Na Kano, Kotun Koli Ta Sanya Ranar Raba Gardama a Shari'ar Zaben Kaduna
- Kwanaki biyu bayan yanke hukuncin zaben jihar Kano, Kotun Koli ta sanya ranar raba gardama a shari'ar zaben Kaduna
- Kotun ta sanya ranar Alhamis 19 ga watan Janairu a matsayin ranar yanke hukuncin karshe kan takaddamar zaben
- Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Uba Sani ya yi nasara a Kotun Daukaka Kara a matsayin halastaccen zababben gwamna a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Kotun Koli ta sanya ranar raba gardama a shari'ar zaben gwamnan jihar Kaduna.
Kotun ta sanar da ranar Alhamis 19 ga watan Janairu a matsayin ranar yanke hukuncin da ake yi a jihar kan zaben gwamna.
Wane hukunci kotun ta yanke a baya?
Isah Ashiru Kudan wanda ya yi takara a jami'yyar PDP shi ke kalubalantar zaben Gwamna Uba Sani na jam'iyyar APC a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kwanakin baya, Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da nasarar Gwamna Uba Sani a matsayin halastaccen zababben gwamna a jihar.
Har ila yau, ta yi fatali da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar PDP, Ashiru Kudan saboda rashin gamsassun hujjoji a shari'ar.
Yaushe aka yanke hukuncin zaben Kano?
Wannan na zuwa ne kwanaki biyu kacal bayan yanke hukuncin zaben gwamnan Kano da ta dauke hankulan mutane a Najeriya baki daya.
A ranar Juma'a ce 12 ga watan Janairu aka tabbatar da nasarar Gwamna Abba Kabir a matsayin halastaccen gwamnan jihar Kano.
Dan takarar jam'iyyar APC, Nasiru Gawuna shi ke kalubalantar zaben da aka gudanar a watan Maris.
A ranar Juma'a ce Kotun Koli ta yanke shari'ar zaben jihohi 8 da suka hada da Kano da Zamfara da Plateau da Bauchi.
Sauran sun hada da jihohin Ebonyi da Legas da Abia da Cross River wanda aka kammala a ranar.
Kotu ta yi hukunci kan shari'ar zaben jihar Kaduna
A wani labarin, Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a Abuja ta yi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Kaduna.
Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Uba Sani na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a Kaduna.
Har ila yau, kotun ta yi fatali da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar PDP, Isa Ashiru Kudan saboda rashin hujjoji.
Asali: Legit.ng