Kotun Daukaka Kara Ta Yi Hukunci a Shari'ar Kakakin Majalisa a Kaduna, Ta Umarci Sake Zabe

Kotun Daukaka Kara Ta Yi Hukunci a Shari'ar Kakakin Majalisa a Kaduna, Ta Umarci Sake Zabe

  • Kitun daukaka kara ta sake rusa zaben kakakin Majalisar jihar Kaduna wanda ya kasance dan jam'iyyar APC
  • Kotun, har ila yau, ta tabbatar da nasarar dan takarar jam'iyyar PDP, Solomon Nuhu a matsayin wanda ya lashe zaben a mazabar Makera
  • Kotun ta umarci sake zabe a wasu mazabu biyar da ke mazabar Makera a cikin jihar saboda samun matsaloli a zaben

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Kotun daukaka kara ta yi hukunci kan shari'ar zaben kakakin Majalisar jihar Kaduna.

Kotun ta kwace kujerar kakakin Majalisar Yusuf Dahiru Liman na jam'iyyar APC inda ta umarci sake zabe a mazabu biyar, cewar Tribune.

Kotu ta kwace kujerar kakakin Majalisar jihar Kaduna, Dahiru Liman
Kotun Daukaka Kara Ta Yi Hukunci a Shari'ar zaben dan Majalisa a Kaduna. Yusuf D. Liman.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun ta yanke?

Kara karanta wannan

APC ta mamaye Majalisar jihar PDP bayan kotu ta kwace dukkan kujeru 16, an shiga yanayi

Dan takarar jam'iyyar PDP a zaben, Solomon Nuhu ya kalubalanci zaben Liman da ke wakiltar mazabar Makera a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nuhu ya ce akwai kura-kurai da aka tafka yayin zaben inda ya tabbatar da cewa shi ya lashe zaben da aka gudanar a watan Maris.

A zaben da aka gudanar, Liman na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 17,740 yayin da takwaransa na jam'iyyar PDP, Nuhu ya samu kuri'u 17,088.

Wasu mazabu za a sake zabe?

Yayin yanke hukuncin, Mai Shari'a, O. Adejumo a ranar Juma'a 24 ga watan Nuwamba ta kori karar da dan jam'iyyar APC ya shigar.

Kotun ta umarci sake zabe a wasu mazabu da su ka hada da Unguwar Barnawa mazaba ta 005 da 009 sai Kakuri a mazabar 006.

Sauran sun hada da Unguwar Television a mazaba ta 002 sai kuma Kakauri Hausa a mazaba 045, cewar Channels TV

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta bayyana ainahin wanda ya lashe zaben gwamnan Kebbi

Kotu ta yi hukunci a shari'ar gwamnan Kaduna

A wani labarin, kotun daukaka kara ta yi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Kaduna da aka gudanar a watan Maris.

Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Uba Sani na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

Har ila yau, ta yi watsi da korafin dan takarar jam'iyyar PDP, Isa Ashiru Kudan saboda rashin gamsassun hujjoji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel