Kotun Koli Ta Yi Hukunci Kan Shari'ar Neman Tsige Gwamnan APC, Bayanai Sun Fito

Kotun Koli Ta Yi Hukunci Kan Shari'ar Neman Tsige Gwamnan APC, Bayanai Sun Fito

  • Yayin da ake ci gaba da yanke hukuncin zaben gwamnoni a Abuja, Kotun Koli ta raba gardama a zaben jihar Ebonyi
  • Kotun ta tabbatar da Gwamna Francis Nwifuru na jami'yyar APC a matsayin halastaccen gwamnan jihar
  • Har ila yau, kotun ta yi fatali da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar PDP, Chukwuma Odili da ke kalubalantar zaben

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kotun Koli da ke birnin Tarayya Abuja ta yi hukunci kan zaben gwamna jihar Ebonyi.

Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Francis Nwifuru a matsayin gwamnan jihar babu tantama, TVC News ta tattaro.

Kotun Koli ta yi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Ebonyi
Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Francis Nwifuru na Ebonyi. Hoto: Francis Nwifuru.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun ta yanke a shari'ar Ebonyi?

Kara karanta wannan

Bayan na Kano, Kotun Koli ta raba gardama kan shari'ar gwamnan PDP a Arewa, ta fadi dalili

Har ila yau, Kotun ta yi fatali da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar PDP, Chukwuma Odili da ke kalubalantar zaben

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar INEC ta tabbatar da Francis Nwifuru na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara a zaben da aka gudanar a watan Maris.

Wannan na zuwa ne bayan Kotun Koli ta tanadi hukunci a shari'ar a ranar Litinin 8 ga watan Janairu a Abuja, kamar yadda Premium Times ta tattaro.

Mene kotun ke cewa kan shari'ar zaben Ebonyi?

Kotun ta saurari dukkan jawaban da mai kalubalantar zaben ya gabatar wanda dan takarar jam'iyyar PDP ne, Chukwuma Odili.

Wanda ya jagoranci alkalan kotun, Mai Shari'a, Tijani Abubakar ya ce Odili da jam'iyyar PDP ba su cika ka'ida ba wurin kalubalantar zaben.

Ya ce hujjojin da su ka kawo ba su kai ruguza zaben ba na neman hana shi takara saboda ya saba dokokin zabe.

Kara karanta wannan

Dauda Vs Matawalle: Kotun ƙoli ta bayyana sahihin wanda ya ci zaben gwamna a jihar Zamfara

Kotu ta tanadi hukunci kan shari'ar Nwifuru

A wani labarin, Kotun Koli ta tanadi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru.

Kotun Daukaka Kara a baya ta tabbatar da nasarar Gwamna Francis Nwifuru na jami'yyar APC a matsayin gwamnan jihar.

Yayin da ta kuma yi fatali da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar PDP, Chukwuma Odili wanda ke kalubalantar zaben da cewa an tafka magudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel