"Burin Kowane Ɗan Najeriya Ya Dauki Hoto da Ni" Ministan Tinubu Ya Yi Magana Mai Jan Hankali

"Burin Kowane Ɗan Najeriya Ya Dauki Hoto da Ni" Ministan Tinubu Ya Yi Magana Mai Jan Hankali

  • Ministan babban birnin tarayya Abuja ya yi ikirarin cewa kowane ɗan Najeriya na son ya ɗauki hoto da shi
  • Nyesom Wike ya bayyana cewa duk da zagi da sukar da ake masa a kafafen sada zumunta, ba haka abun yake ba a fili
  • Ya bada labarin yadda ya cinye taron da shugaban ma'aikatan Bola Tinubu ya shirya a jihar Legas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya (FCT), ya ce kowane dan Najeriya na son daukar hoto da shi.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa ministan ya fadi haka ne a ranar Lahadi a wani liyafar cin abincin rana da ya shirya a Fatakwal, babban birnin Ribas.

Kara karanta wannan

Sanata Ndume ya maida martani kan dakatar da ministar jin kai, ya aike da sako ga Tinubu

Ministan Abuja, Nyesom Wike.
"Burin Kowane Dan Najeriya Ya Dauki Hoto da Ni" Ministan Tinubu Hoto: Nyesom Wike
Asali: Facebook

Wike ya ce 'yan Najeriya suna zaginsa da suka a shafukan sada zumunta, amma idan mutane suka ci karo da shi a wajen bukukuwa ko wuraren taruwar jama'a suna rokon ya ba su damar daukar hotuna da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Idan ka duba shafukan sada zumunta, za ka yi tunanin wannan mutumin shi ne mafi sharrin mutum,” inji shi.

Abin da ya faru da Wike a jihar Legas

Ministan ya bayyana yadda ya ja hankali a wajen taron da Femi Gbajabiamila, shugaban ma'aikatan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya shirya a Legas.

Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas ya ce:

"Ina shiga wurin taron, kowane ɗan Najeriya so yake ya samu damar ɗaukar hoto da ni, har sai da shugaban ma'aikatan ya ce wai kai kaken wannan liyafar ne? Na faɗa masa bani bane, kai fa ka gayyace ni."

Kara karanta wannan

Akwai kitimutmura a 2027: Tawagar G5 ta PDP a ta marawa shugaba Tinubu baya a zaben 2027, Inji Ortom

"Sai da na roƙi Allah kada ya bari matata ta ga waɗan nan hotuna. Ina mamaki ni mutane ke son ɗaukar hoto da ni ko sheɗani ko fatalwa."

Ministan ya ce yana mamakin ko mutane suna ta turereniyar daukar hotuna da shi ne saboda zagin da ake yi masa a shafukan sada zumunta.

Mista Wike ya ƙara da cewa irin wannan lamari ne ya faru ne a gidan shugaban hukumar tara haraji ta kasa FIRS, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Gwamma Bello ya naɗa ciyamomim riko a Kogi

A wani rahoton kuma Gwamna mai barin gado ya naɗa sabbin shugabannin kananan hukumomi na rikon ƙwarya a jihar Kogi

Alhaji Yahaya Bello ya naɗa ciyamomin ne domin cike gurbin da tsoffin shugabannin suka tafi suka bari bayan ƙarewar wa'adinsu

Asali: Legit.ng

Online view pixel