Binciken N37bn: An Wuce Wurin, Hukumar EFCC Ta Dauki Mataki Kan Ministar Buhari, Ta Fadi Dalili

Binciken N37bn: An Wuce Wurin, Hukumar EFCC Ta Dauki Mataki Kan Ministar Buhari, Ta Fadi Dalili

  • A karshe Hukumar EFCC ta sake tsohuwar Ministar jin kai da walwala bisa sharudan ba da beli
  • Farouk ta na hannun hukumar EFCC har kusan awanni 12 tun karfe 11 na safe har zuwa 11:30 na daren jiya Litinin
  • Wannan na zuwa ne bayan zargin badakalar kudade da ake zargin Sadiya da aikatawa yayin da ta ke Ministar jin kai da walwala

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Hukumar EFCC ta ba da belin tsohuwar Ministar Buhari, Sadiya Umar Farouk a ofishinta da ke Abuja.

Farouk ta na hannun hukumar EFCC har kusan awanni 12 tun karfe 11 na safe har zuwa 11:30 na daren jiya Litinin 8 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya ki amsa gayyatar hukumar kula da da’ar ma’aikata

Hukumar EFCC ta dauki mataki kan binciken Ministar Buhari
Hukumar EFCC ta sake Sadiya kan sharudan beli. Hoto: @efccnigeria.
Asali: Facebook

Wane mataki EFCC ta dauka kan Sadiya Farouk?

Jami'an sun mika tambayoyi ga Farouk a gaban lauyanta inda suka bukaci ta yi rubutu kan alakar da ke tsakaninta da dan kwangila, James Okwete.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiya ta tabbatar wa Punch cewa an sake Sadiya a daren jiya bayan hukumar ta ba da belin ta, Premium Times ta tattaro.

Majiyar ta ce:

"Sadiya ta sha tambayoyi kan badakalar tun karfe 11 na safe har zuwa 11:30 ma daren jiya Litinin.
"An sake ta bayan ba da belinta saboda ba za mu rike ta ba kamar yadda ba mu rike Halima Shehu ba saboda ana ci gaba da bincike."

Mene ake zargin Sadiya da aikatawa?

Wannan na zuwa ne bayan zargin badakalar makudan kudade da ake zargin Sadiya da aikatawa yayin da ta ke Ministar jin kai da walwala.

Kara karanta wannan

Jirgin ruwa dauke da fasinjoji 100 ya kife a Neja - NSEMA

Har ila yau, hukumar ta bukaci Sadiya ta sake dawo wa ofishinta yau Talata tare da rubuta bahasi kan alaka da ke tsakaninta da dan kwangila, Okwete.

Ta kuma bai wa Sadiya damar ganin takardun da ke nuna shaidar tura kudaden zuwa asusun bakin Okwete, cewar News Now.

Daga bisani lauyan dan kwangilar, Chukwuemeka Eze ya tabbatar wa 'yan jaridu cewa an sake Okwete.

Jerin mata 7 da ake zargi da badakalar makudan kudade

A wani labarin, Hukumar EFCC na ci gaba da binciken Ministar jin kai da walwala, Betta Edu kan zargin karkatar da wasu kudade.

Har ila yau, Sadiya Umar Farouk, tsohuwar Ministar jin kai na fuskantar bincike kan zargin wawure biliyan 37.

Legit Hausa ta jero muku sunayen wasu mata guda bakwai da ake zargi da almundahana da kudade.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel