An Yi Ta Cece-Kuce Bayan Ministar Tinubu Ta Umarci Tura Mata N585m Ta Bayan Fage, Bayanai Sun Fito

An Yi Ta Cece-Kuce Bayan Ministar Tinubu Ta Umarci Tura Mata N585m Ta Bayan Fage, Bayanai Sun Fito

  • Wata badakala ta sake ballowa bayan fitar da wata takarda inda ta ke nuna yadda Ministar Tinubu ta umarci tura mata wasu kudade
  • Ministar jin kai da walwala, Betta Edu Ta umarci tura mata miliyan 585 zuwa asusun bankin UBA na musamman
  • Legit Hausa ta ji ta bakin wasu da ke cin gajiyar N-Power kan wannan badakala

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – An yi ta cece-kuce bayan Minista Betta Edu Ta umarci tura mata miliyan 585 zuwa asusun banki na musamman.

Edu ta umarci Akanta Janar, Oluwatoyin Sakirat ta tura kudaden yayin da ake zargin Ministar da badakalar biliyoyin kudaden al'umma.

Wata sabuwar badakalar kudade ta kunne kai kan Minsitar Tinubu
Ministar Tinubu Ta Umarci Tura Mata N585m Ta Bayan Fage. Hoto: Dr. Betta Edu.
Asali: Facebook

Wane umarni Ministar Tinubu ta bayar?

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Mutum uku da aka sace sun mutu a kokarin gudowa daga hannun yan bindiga

Umarnin biyan kudaden ya fito fili ne a cikin wata takarda da TheCable ta leko a ranar 20 ga watan Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Takardar wacce Ministar ta sanya wa hannu na dauke da rubutu kamar haka:

“Umarnin biyan kudaden marasa karfi a jihar Akwa Ibom da Cross River da Legas da kuma Ogun.”

A cikin takardar, Edu ta umarci Akanja Janar ta tura kudaden har naira miliyan 585 zuwa asusun bankin UBA mai dauke da sunan Oniyelu Bridget Mojisola.

Kamar yadda takardar ta fito naira miliyan 219 an ware su don taimakon marasa karfi a 2023 a jihar Akwa Ibom sai miliyan 73 a jihar Cross River.

Wace sanarwa takardar ke dauke da shi?

Har ila yau, an ware naira miliyan 219 saboda jihar Legas sai kuma naira miliyan 72 don jihar Ogun, cewar Peoples Gazette.

Kara karanta wannan

Gungun matasa sun cinna wa gidan yayar mai sarautar gargajiya a Arewa wuta, ta rasu da jikarta

Sanarwar ta ce:

“Ina umartar biyan kudade naira miliyan 585 daga asusun tallafawa marasa karfi don inganta rayuwarsu.
“Biyan kudaden za a yi su ne daga asusun hukumar walwalar jama’a ta kasa kamar haka 0020208461037.”

Fitar da wannan takarda ya jawo martanin jama’a da dama a Najeriya inda mutane suka saka alamar tambaya kan wannan umarni.

Legit Hausa ta tattauna da wasu da ke cikin shirin N-Power kan lamarin:

Hassan Abdullahi ya ce daman ta nan kudadensu suka makale musamman tun lokacin Sadiya Umar Farouk.

Ya yaba wa Shugaba Tinubu kan wannan kokari da ya ke yi kan yaki da cin hanci.

Muhammad Abubakar wanda ke bin bashin watanni da dama ya ce:

"Abin takaici ne yadda aka hana mu hakkin mu ashe ga ta inda kudaden suke makale wa."

Ya koka kan yadda Edu da ake mata kyakkyawan zato zata karkatar da wadannan kudaden taimakon marasa karfi.

Kara karanta wannan

NSCDC ta kama fasto da wasu mutane biyu kan damfara a Kogi

Sadiya ta fadi dalilin kin amsa gayyatar EFCC

A wani labarin, Tsohuwar Minsitar jin kai da walwala, Sadiya Umar Farouk ta bayyana ddalilin kin amsa gayyatar da aka yi mata zuwa EFCC.

Sadiya ta tura takarda hukumar inda ta ke neman karin lokaci saboda rashin lafiyar da take fama da ita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel