Takarar 2023: Abin da Ya Taimaki Tinubu a Kan Amaechi, Osinbajo da Lawan Inji Jagoran APC

Takarar 2023: Abin da Ya Taimaki Tinubu a Kan Amaechi, Osinbajo da Lawan Inji Jagoran APC

  • Salihu Lukman ya ce tarihin Bola Ahmed Tinubu a tafiyar siyasa ta ba shi damar zama ‘dan takaran APC a zaben 2023
  • Watanni da zabe da kuma nasarar jam’iyya mai-ci, jigon na APC yana ganin har yanzu ba a samu yadda ake so a mulki ba
  • Dr. Lukman ya ce dole sai gwamnati ta dage domin cin ma manufar APC, sannan ana bukatar ayi gyara a jam’iyyun siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Tsohon shugaban kungiyar PGF ta gwamnonin jihohin APC, Salihu Lukman ya yi bayani game da takarar Bola Ahmed Tinubu.

Dr. Salihu Lukman ya yi rubutu inda ya tabo maganar yadda aka tsaida Bola Ahmed Tinubu takara, The Guardian ta kawo rahoton nan.

Kara karanta wannan

An kawo wata dabarar tsige Gwamnan PDP, Magoya bayan Minista ba su hakura ba

Shugaba Bola Tinubu
Shugaban kasa Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Ficen Bola Tinubu a siyasa

‘Dan siyasar ya yi rubutu ne a kan abin da ya shafi yadda za a gyara jam’iyyu, a nan ya yabi salon siyasar Mai girma sabon shugaban Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Salihu Lukman yake cewa zaman Bola Tinubu asalin wanda ya san tsarin damukaradiyya ya taimaka masa wajen samun tikitin APC.

Tsohon mataimakin shugaban na APC a shiyyar Arewa maso yamma yake cewa tsohon gwamnan yana da dogon tarihi idan ana batun siyasa.

Wannan ya taimaki Tinubu har aka tsaida shi a matsayin ‘dan takara a kan duk sauran wadanda su ka nemi tutar APC wajen zaben bana.

An rahoto Dr. Lukman ya ce zai kaddamar da littafi da ya rubuta a kan siyasar jam’iyyar APC da aka kafa a 2013 da yadda ta samu mulki.

Kara karanta wannan

Kamar Wasa: Masoyin Buhari ya rubuta masa gayyatar aure, kati ya isa gare shi a Daura

Bola Tinubu ya saki layin APC?

Amma kuma bayan hawa mulki, marubucin ya zargi shugaba Tinubu da kauce hanyar da wadanda su ka kafa jam’iyyarsu ta APC su ka tsara.

Lukman ya ce babu abin da zai hana shi fitowa yana kiran shugabanni su yi mulki na kwarai, sannan a kawo sauyi wajen tsarin jam’iyyun siyasa.

Idan an samu matsala a gwamnatin Muhammadu Buhari, Lukman ya ce bai kamata a mulkin Bola Tinubu, APC ta saki layi daga kan manufarta ba.

Amma ‘dan siyasar yana ganin cewa har yau ana nan a gidan jiya, yake cewa da alama siyasar gwamnatin Tinubu ta sa a gaba ba yin mulki ba.

...Tinubu ya yi nadin mukamai

Wata sanarwa daga fadar shugaban Najeriya ta fito cewa Mista Felix Ogbe ya zama sabon shugaban NCDMB kuma an nada shugabanni a NPC.

Ajuri Ngalele ya ce sauran wadanda aka ba mukamai a hukumar sun hada da Oritsemyiwa Eyesan, Gbenga Komolafe da Olorundare Thomas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel