Ekiti: Jam'iyyar APC Ta Lashe Zaben Kananan Hukumomi 38 da Kansiloli 177 a Jiha Ɗaya

Ekiti: Jam'iyyar APC Ta Lashe Zaben Kananan Hukumomi 38 da Kansiloli 177 a Jiha Ɗaya

  • Hukumar zaɓe ta jihar Ekiti ta sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi da aka yi ranar Asabar, 2 ga watan Disamba, 2023
  • Shugaban hukumar, Cornelius Akintayo, ya ce jam'iyyar APC ta lashe dukkan kujerun ciyamomi 38 da kansiloli 177
  • Babbar jam'iyyar adawa PDP tare da jam'iyyar SDP ba su shiga zaben ba wanda jam'iyyu takwas suka fafata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ekiti - Jam'iyyar All Progressive Congress (APC) ta lashe dukkan kujerun shugabannin kananan hukumomi 38 da na kansiloli 177 a zaben da aka yi a jihar Ekiti.

Rahoton The Nation ya nuna cewa a ranar Asabar, 2 ga watan Disamba, 2023 aka gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnan Bauchi Bala Mohammed ya yi ganawar sirri da Wike kan zaben 2027, rahoto

Jam'iyyar APC ta lashe zaben kananan hukumomi a Ekiti.
Jam'iyyar APC Ta Lashe Zaben Ciyamomi da Kansiloli a Jihar Ekiti Hoto: OfficialAPC
Asali: UGC

Zaben ya gudana ne a dukkanan kananan hukumomi 16 da yankunan ci gaba 22 da kuma mazaɓun kansiloli 177 da ke faɗin jihar Ekiti.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda sakamakon zaben ya kasance

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Ekiti ce ta sanar da sakamakon zaben ranar Lahadi, 3 ga watan Disamba, 2023 a Ado Ekiti, babban birnin jihar.

Da yake sanar da sakamakon, shugaban hukumar zaɓen, mai shari'a Cornelius Akintayo mai ritaya, ya ce APC ta samu nasarar lashe kujerun ciyamomi 38 da kansiloli 177.

Akintayo ya kuma bayyana cewa zaben ya gudana bisa tsari da bin tanade-tanaden kundin dokokin zaben Ekiti, cewar rahoton Leadership.

Ya ƙara da yabawa ɗaukacin al'ummar jihar bisa yadda suka fito kuma suka bada haɗin kai wajen ganin zaɓen ya gudana lami lafiya.

Ya kuma yabawa jam’iyyun siyasa takwas da suka fafata a zaben kan yadda suka bada haɗin kai, sannan ya jinjinawa jami’an zabe da suka nuna kwarewa wajen gudanar da zaben.

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya kunno PDP yayin da Atiku da fitaccen gwamna suke neman iko, karin bayani

Jam'iyyun da suka gwabza a zaɓen Ekiti

Jam'iyyun da suka shiga cikin takardun kaɗa kuri'a suka fafata a zaben sun haɗa da APC, AA, ADP, NNPP, ADPP, Labour Party, PRP da ZLP.

A ɗaya bangaren kuma babbar jam'iyyar adawa People Democratic Party (PDP) da kuma Social Democratic Party (SDP) sun ƙauracewa zaɓen na ranar Asabar.

An gano waɗanda suka saki bam a taron Maulidi

A wani labarin kuma Rundunar sojojin ƙasa ta Najeriya ta ɗauki alhakin harin bam ɗin da aka kai kan mahalarta taron Maulidi ranar Lahadi a Kaduna.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, shi ne ya tabbatar da haka a ƙarshen taron majalisar tsaro ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel