Gwamnan Ekiti Oyebanji Ya Kaiwa Tsohon Telansa Ziyarar Bazata, Hotunan Sun Yadu

Gwamnan Ekiti Oyebanji Ya Kaiwa Tsohon Telansa Ziyarar Bazata, Hotunan Sun Yadu

  • Gwamna Biodun Oyebanji na jihar Ekiti ya kaiwa tsohon telansa ziyarar bazata a Ado-Ekiti, inda ya yi karatu a jami'ar jihar Ondo, jami'ar jihar Ekiti a yanzu
  • Gwamnan ya bayyana jin dadinsa ga Mista David Aina, wanda ke yi masa dinki lokacin da yake karatun digiri
  • Yan Najeriya a soshiyal midiya sun jinjinawa wannan ziyara, inda suka yaba ma gwamnan kan wannan karamci nasa da tuna baya

Ado-Ekiti, Jihar Ekiti - Gwamna Biodun Oyebanji na jihar Ekiti ya kai ziyarar bazata ga tsohon telansa da ke yi masa dinki lokacin da yake makaranta a jami'ar jihar Ondo a Ado Ekiti wanda ya zama jami'ar jihar Ekiti a yanzu.

Gwamnan ya wallafa hotunan ziyarar da ya kai wa mai dinkin nasa Davis Aina a shafinsa na Facebook a ranar Juma'a, 13 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Ayiriri: Ɗan Majalisar Tarayya Ya Yi Wuff da Fitacciyar Yar Kasuwar Nan a Arewa Laylah Othman

Gwamnan Ekiti ya ziyarci tsohon telansa
Gwamnan Ekiti Oyebanji Ya Kaiwa Tsohon Telansa Ziyarar Bazata, Hotunan Sun Yadu Hoto: Biodun Oyebanji
Asali: Facebook

Ya bayyana ziyarar a matsayin tafiyar tuna baya wanda ya ba shi damar haduwa da wani mutum wanda ya taka rawar gani a rayuwarsa.

"Na kai ziyarar bazata ga Mista David Aina, shahararren tela wanda ke da kamfanin Davis Cuts Fashion House, da ke kusa da Oluyemi Kayode Stadium a Ado-Ekiti," inji shi."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mista David yana da wuri mai girma a zuciyana, a matsayinsa na tela da na fi wanda ke dinka mun kayana a lokacin da nake karatu a jami'ar jihar Ondo a Ado-Ekiti, (jami'ar jihar Ekiti a yanzu) ziyarar ya kasance na tuna baya, sake haduwa da mutumin da ya taka muhimmiyar rawar gani a rayuna na baya kuma ya ci gaba da haskawa a duniyar ado."

Yan Najeriya sun yi martani ga ziyarar da gwamna ya kaiwa tsohon telansa

Ajayi Dauda Opeyemi ya ce:

Kara karanta wannan

An Kama Dan Kasuwa a Kano Kan Hada Baki Da Wasu Mutane 2 Don Yi Wa Abokinsa Fashi

"Misali mai kyau daga shugaba nagari. Wannan shine dalilin da yasa gwamna mazauni gida ya fi. Shakka babu mutanen Ekiti sun yi daidai a wannan karon. Ka ci gaba da daga tutar yallabai.

Ayodeji Daniel Agunbiade ya ce:

"Wayyo ni, mutumin ne yake yiwa marigayi mahaifina dinki. Na tuna marigayi mahaifina yana kaini shagon nan don a gwada ni. Wow! Wannan irin karamci daga gwamnan!"

John Bamigboye ya ce:

"Kai mutumin kirki ne mai girma gwamna! Ina kaunarka kan kowani aiki na kankan da kai da nuna soyayya. Don Allah, ka ci gaba da haka Yallabai."

Dan majalisar tarayya ya yi wuff da shahararriyar yar kasuwa, Laylah Othman

A wani labari na daban, mun ji cewa Shahararriyar 'yar kasuwar nan ta arewa wacce ta yi fice a bangaren kayan alatu da kawata gida, Laylah Ali Othman ta shiga daga ciki.

An daura auren Laylah da angonta, Yusuf Gagdi, wanda ya kasance dan majalisar tarayya mai wakiltan mazabar Pankshin/Kanke/Kanam ta jihar Filato a ranar Juma'a, 13 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel