Kaduna: Rundunar Sojin Ƙasa Ta Ɗauki Laifi, Ta Faɗi Gaskiyar Abinda Ya Jawo Jefa Bam a Taron Maulidi

Kaduna: Rundunar Sojin Ƙasa Ta Ɗauki Laifi, Ta Faɗi Gaskiyar Abinda Ya Jawo Jefa Bam a Taron Maulidi

  • A ƙarshe, rundunar sojin kasa ta Najeriya ta ɗauki laifin harin bam ɗin da aka kai kan bikin Maulidi ranar Lahadi a Kaduna
  • Kwamandan runduna ta ɗaya, Manjo VU Okoro, ya yi bayanin yadda jami'an soji suka yi kuskure yayin kai samame kan yan bindiga
  • A wata sanarwa, gwamnatin Kaduna ta aike da sakon ta'aziyya ga dangin waɗanda suka rasa rayukansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Rundunar sojojin ƙasa ta Najeriya ta ɗauki alhakin harin bam ɗin da aka kai kan mahalarta taron Maulidi ranar Lahadi a kauyen Tudun Biri a jihar Kaduna.

Rundunar ta bayyana cewa ba da nufi ta saki bam kan taron Maulidi ba, inda ta ƙara da bayanin cewa jami'anta na aikin kai hari maɓoyar yan ta'adda ne lokacin da suka yi kuskuren.

Kara karanta wannan

Rundunar sojin sama ta yi martani kan zargin kai harin bam kan masu Maulidi a Kaduna, ta roki jama'a

Jirgin sojojin Najeriya.
Yanzun Nan: Gwamnatin Kaduna Ta Bayyana Jami'an Tsaron da Suka Kai Harin Bam a Taron Maulidi Hoto: Nigerian Air Force HQ
Asali: UGC

Daily Trust ta ce kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, shi ne ya tabbatar da haka a ƙarshen taron majalisar tsaro na gaggawa ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan baku manta ba mun kawo muku rahoton yadda wani jirgin sojojin Najeriya ya yi kuskuren sakin bam a taron Maulidi, lamarin da ya yi ajalin mutane da dama.

Bayanai sun nuna akalla mutane 30 da suka halarci Maulidin ake fargabar sun mutu sakamakon wannan harin na sojoji.

Sai dai kwamishinan ya bayyana cewa rundunar sojojin ƙasa ta ɗauki alhakin cewa jami'anta ne suka tafka wannan kuskuren a jihar Kaduna, Channels tv ta ruwaito.

Yadda sojoji suka yi kuskuren jefa bam kan yan Maulidi

A sanarwan da ya fitar, Aruwan ya ce:

"Gwamnatin Kaduna ta samu rahoton harin bam ɗin da aka kai jiya Lahadi da daddare wanda ya yi ajalin mutane da dama a taron da mataimakiyar gwamna, Hadiza Balarabe ta jagoranta."

Kara karanta wannan

Sojoji sun saki bam sun kashe mutane a wajen Maulidin Annabi SAW a Kaduna

"Shugabannin hukumomin tsaro, sarakuna da shugabannin addinai sun halarci taron, inda rundunar sojin ƙasa ta yi bayanin yadda lamarin ya faru bisa kuskure."
"Kwamandan rundunar soji ta ɗaya, Manjo VU Okoro, ya yi bayanin cewa jami'an soji na aikin yaƙi da 'yan ta'adda kamar yadda suka saba bisa kuskure suka taɓa mutanen kauyen."

Daga karshe, mataimakiyar gwamnan ta miƙa sakon ta'aziyya a madadin gwamnatin Kaduna ga dangin waɗanda suka rasa rayukansu.

Rundunar Sojin Sama Ta Yi Martani Kan Zargin Kai Harin Bam

A wani rahoton na daban Yayin da ake cikin tashin hankali na harin bam kan masu Maulidi, rundunar sojin sama ta yi martani kan lamarin.

Rundunar ta karyata labarin da ake yadawa inda ta ce babu kamshin gaskiya a ciki, ta kuma bukaci ayi watsi da labarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel