Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya koma PDP

Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya koma PDP

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party PDP a yau Juma’a 19 ga watan Yuni, 2020, Legit Hausa ta samu rahoto.

Gwamna ya alanta sauya shekarsa ne a hedkwatan jam'iyyar PDP ta jihar Edo dake `Benin City, abbar birnn jihar ranan nan.

Ya ce yana da masaniyar nauyin da ya hau kansa yanzu da ya koma jam'iyyar saboda daga yanzu shine uban dukkan 'yayan jam'iyyar a Edo.

Ya ce ba tare da bata lokaci ba, zai garzaya rijista bisa ka'ida a matsayin sabon dan jam'iyya.

Gwamna Obaseki ya samu rakiyar dimbin mabiya da masoyansa.

Gwamnan da kansa ya bayyana hakan a shafin na Tuwita inda yace:

"Na sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP domin cigaba da manufata na saken takaran neman kujeran gwamnan jihar Edo."

"Kamar yadda na saba, zan cigaba da tabbatar da mulkin kwarai da kawo cigaba ga jiharmu."

Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya koma PDP
Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya koma PDP
Asali: Depositphotos

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel