Gwamna Obaseki Ya Hana Mataimakinsa Philip Shaibu Shiga Ofis

Gwamna Obaseki Ya Hana Mataimakinsa Philip Shaibu Shiga Ofis

  • Rikicin da ake a tsakanin gwamna Godwin Obaseki da mataimakinsa, Philip Shaibu, ya ƙara kamari
  • Hakan ya faru bayan an hana Shaibu ya shiga ofishinsa da ke gidan gwamnatin jihar a birnin Benin, ranar Litinin, 18 ga watan Satumba
  • Wannan dai shi ne rikici na baya-bayan nan da ya ƙara ɓarkewa a tsakanin gwamna Obaseki da Shaibu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Birnin Benin, jihar Edo - Rikicin siyasar da ake yi a gidan gwamnatin jihar Edo ya ɗauki wani sabon salo.

Jaridar Channels Tv ta rahoto cewa an hana mataimakin gwamnan jihar Edo Philip Shaibu shiga tsohon ofishinsa na gidan gwamnatin jihar da ke birnin Benin, babban birnin jihar.

Gwamna Obaseki ya hana mataimakinsa shiga ofis
Gwamna Obaseki ya hana Philib Shaibu shiga ofishinsa a gidan gwamnatin jihar Edo Hoto: Governor Godwin Obaseki
Asali: Facebook

Rahotanni sun ce Shaibu ya isa gidan gwamnati ne a safiyar ranar Litinin, 18 ga watan Satumba, amma sai ya tarar an kulle ƙofar da za ta sada shi zuwa cikin ofishinsa.

Kara karanta wannan

Ana zaman dar-dar: Gini ya ruguje kan jama'a, mutum 2 suna can jina-jina a asibiti

Ya ce har yanzu bai samu takarda ba daga ofishin gwamna Godwin Obaseki kan sauya masa ofis, inda a cewarsa ita ce hanyar da ta dace ya samu umarnin sauya ofis.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shaibu a yayin da yake magana da wani wanda ba a san kowane ne ba, ta wayar tarho ya bayyana cewa:

"Har ya zuwa yanzu, ba a sanar da ni a hukumance cewa an sauya min ofis ba. Ma'aikata na ne kawai waɗanda aka sanar a hukumance. Ma'aikatan an sanar da su a hukumance, amma ni ba a sanar da ni ba. A yanzu haka da na ke magana da kai, ina tsaye a bakin ƙofa."

A yayin da ake ta raɗe-raɗi kan kan shirin tsige Shaibu, majalisar dokokin jihar ta musanta hakan.

Mataimakin Gwamna Shuaibu Ya Fice Daga Gidan Gwamnati

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan Bindiga Sun Tarwatsa Garuruwan Noma 15 a Arewa, Sun Raba Mutane da Amfanin Gonakinsu

Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shuaibu ya fara tattara kayansa daga gidan gwamnati zuwa wani sabon ofishi.

Shuaibu na shirin tattara kayansa ne zuwa wani da ke nesa da gidan gwamnatin jihar.

Shehu Sani Ya Fadi Jam'iyyar Da Za Ta Ci Ribar Rikicin Obaseki da Shaibu

A wani labarin kuma, tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yi tsokaci kan rikicin da ke a tsakanin gwamna Obaseki da Philip Shaibu.

Tsohon sanatan ya bayyana cewa jam'iyyun APC ko Labour Party ne za su ci ribar faɗan da ake yi a tsakanin gwamnan da mataimakinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel