Edo: Ubangiji Ne Ya Umurce Ni In Nemi Kujarar Gwamna, In Ji Shaibu

Edo: Ubangiji Ne Ya Umurce Ni In Nemi Kujarar Gwamna, In Ji Shaibu

  • Philip Shaibu, mataimakin gwamnan jihar Edo ya bayyana dalilin da ya sa ya tsaya takarar gwamnan jihar a zaben 2024 mai zuwa
  • Shaibu ya ce ba ya aikata komai don kashin kansa, wannan takarar ubangiji ne ya ce masa ya yi ta don kwato hakkin mutanensu
  • Da yake jawabi na tsayawarsa takara a hukumance, Shaibu ya ce babu wani mahaluku da ya isa ya dakatar da shi daga wannan kudiri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Edo - Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu ya danganta burinsa na tsayawa takarar gwamna a jihar a zaben 2024 da 'samun umarni daga Allah'.

Shaibu ya ce ya yi shawara da ubangiji kuma ya samu sako karara domin ci gaba da shirinsa na takarar gwamnan jihar.

Kara karanta wannan

Rigima ta ɓalle, Mataimaki Shaibu ya ɗara caccakar Gwamnan PDP kan zaben jihar na 2024

Hon Philip Shaibu/Jihar Edo/Kujerar gwamna
Shaibu ya ce Allah yana tare da shi don haka babu wanda ya isa ya dakatar da shi daga neman kujerar gwamnan Edo. Hoto: @HonPhilipShaibu
Asali: Twitter

A ranar Litinin ne Shaibu ya bayyana a hukumance cewa zai tsaya takarar gwamnan jihar a zaben 2024 a karkashin jam’iyyar PDP, Premium Times ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babu wanda ya isa ya hana ni takarar gwamna - Shaibu

Shaibu dai ya sha takun saka tsakaninsa da maigidansa Gwamna Godwin Obaseki kan burinsa amma daga baya kurar rigimar ta lafa.

Da yake magana a gidan talabijin na a ranar Talata, Daily Trust ta ruwaito mataimakin gwamnan na cewa:

“Abin da nake nufi shi ne ba wanda zai iya dakatar da mu, mu mutanen Edo ne, wannan wata fafutuka ce ta kwato hakkinmu.
“Don haka lokacin da na ce babu wanda zai iya hana ni, eh, babu wani mahaluki domin na yi imani da ubangiji kuma na san shi kadai ne yake da ikon hana wani abu daga faruwa."

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan Kano, Bello, ya bayyana abu 1 tak da ke sa shi farin ciki a rayuwarsa

Allah ne ya yarje mun in nemi takarar gwamna - Shaibu

Ya kara da cewa:

“Mutane ba za su iya hana wani abu daga faruwa ba saboda ubangiji ya ba mu madafun iko ne don wasu dalilai.
“Ubangiji da ya ke ba da talauci shi ne wanda ya yarje mun na nemi takara, ba na yin abu don kashin kaina don haka tunda na tabbata ubangiji yana tare da ni, babu mai iya hana ni.”

Obaseki ya sauya wa Shaibu ofis

A wani labarin da Legit Hausa ta ruwaito, rikici tsakanin gwamna da mataimakinsa ya kara tsananta a jihar Edo, gwamnati ta sauya wa Shaibu ofis.

Ga dukkan alamu gwamnatin Obaseki na shirin fitar da mataimakin gwamna daga gidan gwamnati zuwa wani wuri daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel