Zaben 2023: Sai da NNPP Ta Tafka Magudi Sannan Ta Samu Nasara a Kano, Ado Doguwa

Zaben 2023: Sai da NNPP Ta Tafka Magudi Sannan Ta Samu Nasara a Kano, Ado Doguwa

  • Dan majalisar mazabar Tudun Wada/Doguwa ya zargi jam'iyyar NNPP ta tafka magudi a zaben gwamnan jihar da ya gudana a 2023
  • Ahassan Ado Doguwa ya ce NNPP ta yi amfani da kuri'un bogi wajen yin aringizon kuri'u wanda ya ba jam'iyyar nasara a zaben 18 ga watan Maris
  • Dan majalisar ya fadi haka ne a lokacin da ya ke martani kan shari'ar Kano, inda ya ce korar Abba alama ce ta bankado magudin da NNPP ta tafka a Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kano - Tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar tarayya, Alhassan Ado Doguwa ya yi ikirarin cewa jam'iyyar NNPP ta tafka magudi a zaben jihar na 2023.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta tsige dan majalisar PDP a jihar arewa, ta daura dan takarar APC a kujerar

Ado Doguwa wanda dan majalisa ne yanzu mai wakiltar mazabar Tudun Wada/Doguwa daga jihar Kano, ya ce NNPP ta yi amfani da kuri'un bogi a zaben.

Alhassan Ado Doguwa/Zaben Kano/Jam'iyyar NNPP
Dan majalisar ya ce NNPP ta yi amfani da kuri'un bogi wajen samun nasara a zaben 2023. Hoto: @aadoguwa
Asali: Twitter

Idan ba a manta ba, Legit Hausa ta ruwaito maku cewa NNPP ta samu kuri'u mafi rinjaye a zaben shugaban kasa da kuma lashe kujerun majalisar tarayya da da dama a babban zaben 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke kan zaben Kano

Haka zalika hukumar INEC ta ayyana NNPP a matsayin wacce ta lashe zaben gwamnan Kano da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris, da samun mafi rinjaye a majalisar dokokin jihar.

Sai dai, kotun sauraron kararrakin zabe ta kwace nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf na NNPP a watan Satumba, inda ta ayyana Nasir Yusuf Gawuna na APC matsayin halastaccen gwamna.

Kara karanta wannan

Jami’an Tsaro sun cika ko ina, NNPP da APC sun hakura da zanga zanga a Kano

Kin amincewa da wannan hukunci, Gwamna Abba da NNPP suka daukaka kara, inda ita ma Kotun Daukaka Karar ta tabbatar da hukuncin kotun zaben Kano na korar Gwamna Abba.

Me Alhassan Ado Doguwa ke cewa kan nasarar NNPP a Kano?

Da ya ke martani kan shari'ar a gidan talabijin na Channels a ranar Laraba, Doguwa, jigon jam'iyyar APC ya ce hukuncin kotun biyu ya tabbatar da irin magudin da NNPP ta tafka a Kano.

Ya ce jam'iyyar NNPP ta samu nasarar a mazabu da dama saboda tana da kuri'un bogi a mallakinta, wanda ta yi amfani da su wajen cin zaben, rahoton jaridar Leadership.

Sai dai Doguwa, ya kare kansa kan wannan ikirari na cewa NNPP ta yi amfani da kuri'un bogi a yayin da ake gudanar da zaben gwamnan jihar na 2023.

Mahaifiyar rikakken dan daba a Kano ta mika shi hannun 'yan sanda

Kara karanta wannan

PDP ta kara shiga matsala yayin da kotun daukaka kara ta tsige yan majalisa 11 a jihar Filato

A wani labarin, Mahaifiyar rikakken dan daba da ake nema ruwa a jallo a jihar Kano, ta yi ta-maza inda ta mika shi ga 'yan sandan jihar a ranar Talata, Legit Hausa ta ruwaito.

A baya-bayan nan ne rundunar 'yan sanda ta fitar da sanarwar sanya kyautar naira dubu dari biyar ga duk wanda ya gano inda dan dabar mai suna Hantar Daba ya ke.

Asali: Legit.ng

Online view pixel