Kotun Daukaka Kara Ta Tsige Dan Majalisar PDP a Jihar Arewa, Ta Daura Dan Takarar APC a Kujerar

Kotun Daukaka Kara Ta Tsige Dan Majalisar PDP a Jihar Arewa, Ta Daura Dan Takarar APC a Kujerar

  • An tsige dan majalisar PDP, Hon Suleiman Wanchiko, wanda ke wakiltar mazabar Bida 1 (Arewa) a majalisar dokokin jihar Neja daga kujerarsa
  • Kotun Daukaka Kara da ke zama a Abuja ta yarda cewa bai kamata a bari Wanchiko ya yi takara a zaben ba kasancewar ya gabatarwa INEC da satifiket na bogi
  • Kotun ta ayyana Bako Kasim na jam'iyyar APC mai mulki a matsayin wanda ya lashe zaben

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

FCT, Abuja - Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a Abuja ta tsige Hon Suleiman Wanchiko mai wakiltar mazabar Bida I (Arewa) a jihar Neja.

Kwamitin kotun mai mutum uku karkashin jagorancin Mai shari'a Bature Isa-Gafai ya ayyana Bako Kasim na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben dan majalisar jihar.

Kara karanta wannan

APC ta mamaye Majalisar jihar PDP bayan kotu ta kwace dukkan kujeru 16, an shiga yanayi

Kotun daukaka kara ta tsige dan majalisar PDP a Neja
Kotun Daukaka Kara Ta Tsige Dan Majalisar PDP a Jihar Arewa, Ta Daura Dan Takarar APC a Kujerar Hoto: Gov Sule Abdullahi Mandate
Asali: Facebook

Kotun Daukaka Karar ta tabbatar da cewar karar da dan takarar PDP, Wanchiko ya daukaka bata da inganci, rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai shari'a Isa-Gafai ya yarda cewa bai kamata a bari Wanchiko ya yi takara a zaben ba kasancewar ya gabatarwa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) da takardar bogi.

Wanchiko, ta hannun lauyansa, Aliyu Lemu, SAN, ya tunkari Kotun Daukaka Kara bayan an yi umurnin sake zabe ba tare da shi ba, rahoton Daily Post.

Kotun ta yanke hukunci cewa bayan tsige Wanchiko, hukuncin da ya dace shine ayyana Kasim a matsayin wanda ya lashe zaben tare da umurtan hukumar INEC da ta ba shi takardar shaidar cin zabe.

Kotu ta tsige yan majalisa 11 a Filato

A wani labari makamancin wannan, mun kawo a baya cewa kotun daukaka kara da ke zama a Abuja, ta tsige yan majalisa 11 na jam'iyyar PDP a majalisar dokokin jihar Filato a ranar Juma'a, 24 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

PDP ta kara shiga matsala yayin da kotun daukaka kara ta tsige yan majalisa 11 a jihar Filato

A wani hukunci na bai daya, kwamitin kotun karkashin jagorancin Mai shari'a Okon Abang, ya tabbatar da cewar dukkan yan majalisar da aka tsige sun samu kuri'u marasa amfani a zabenna watan Maris saboda jam'iyyarsu bata da tsari, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Ya kara da cewar jam'iyyar PDP ta saba sashi na 177 na kundin tsarin mulkin 1999, saboda haka ba za ta iya daukar nauyin yan takara a zabe ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel