Jigon PDP, Nyesom Wike Ya Hadu da Ganduje a ‘Shirin’ Sauya Sheka Zuwa APC

Jigon PDP, Nyesom Wike Ya Hadu da Ganduje a ‘Shirin’ Sauya Sheka Zuwa APC

  • Abdullahi Umar Ganduje ya karbi bakuncin Nyesom Wike a gidansa a birnin tarayya na Abuja
  • Sabon shugaban na APC ya ce Ministan goben ya zo taya shi murna ne na zama shugaban jam’iyya
  • Ziyarar za ta kada hantar ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP da su ke jin haushin tsohon Gwamnan na Ribas

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Nyesom Wike ya kai ziyara zuwa gidan shugaban jam’iyyar APC na kasa, ya kuma zauna da Abdullahi Umar Ganduje.

Rahotanni da hotuna da su ka fito daga shafin Dr. Abdullahi Umar Ganduje a Facebook sun tabbatar da ziyarar a ranar Talata.

Watakila Nyesom Wike wanda ya yi wa jam’iyyar APC aiki a zaben shugaban kasa na 2023, ya na shirin sauya-sheka ne a siyasa.

Abdullahi Umar Ganduje da Nyesom Wike
Shugaban APC da Nyesom Wike Hoto: Abdullahi Umar Ganduje OFR
Asali: Facebook

Meya kai Wike wajen Ganduje?

Aminu Dahiru Ahmad wanda shi ne mai daukar hoton shugaban APC na kasa ya dauki hoton haduwar da kuma zaman da aka yi.

Kara karanta wannan

Muddin Aka Sake Kara Farashin Fetur, Za Mu Birkita Kasar Nan da Yajin Aiki Inji NLC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A jawabin da aka fitar, Ganduje ya shaida cewa ministan goben ya zo taya shi murnar zama sabon shugaban APC ne a gidansa.

Wike: Ministan gobe zai shiga APC?

Ziyarar ta zo ne ‘yan kwanaki kafin rantsar da Wike a matsayin minista a gwamnatin tarayya bayan tantance shi a majalisa.

Tsohon gwamnan na jihar Ribas fitaccen ‘dan jam’iyyar adawa ta PDP ne, amma Bola Ahmed Tinubu ya zabe shi cikin ministocinsa.

Daily Trust ta ce jita-jitar barin PDP ta kara karfi da aka ji Mista Wike a sunayen ministoci, mukamin da ya bari a shekarar 2014.

Watakila lamarin ba zai yi wa jagororin jam’iyyar hamayya ta PDP dadi ba, wasu su na zarginsa da cin amanar Atiku Abubakar.

PDP za ta rasa jihar Ribas?

Kara karanta wannan

Shugaba a APC Ya Rubutawa Tinubu Wasika, Ya ce ‘Gwamnatinka Ta Ba Mu Kunya’

A wajen bikin ban-kwana da aka shirya masa a coci bayan ya mika mulki, ‘dan siyasar ya nuna yiwuwarsa ya bi APC mai mulki.

Wike ya bukaci magajinsa a Ribas, Gwamna Simi Fubara da cewa ka da ya yi watsi da shi ko ya samu kan shi a jam’iyya mai-mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel