Buhari Ya Ambaci Babban Rauni 1 da Yake da Shi Wanda Ya Iya Kawo Cikas a Mulkinsa

Buhari Ya Ambaci Babban Rauni 1 da Yake da Shi Wanda Ya Iya Kawo Cikas a Mulkinsa

  • Muhammadu Buhari ya samu lokaci ya yi hira da ‘yan jarida watanni bayan ya sauka daga karagar mulki
  • Tsohon shugaban kasar ya bayyana kalubalen da ya samu wajen jagorantar Najeriya na shekaru takwas
  • Buhari ya ce muddin ya ba mutum wata kujera, to zai rabu da shi ne ya sauke nauyin da aka daura masa

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Katsina - Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya nanata cewa ya yi bakin kokarinsa a shekaru takwas da ya yi a ofis.

Amma duk da kokarin da yake ganin ya yi a kan mulki, This Day ta rahoto shugaban ya na mai cewa bai san ko ya iya cin ma nasara ba.

Kara karanta wannan

“Da na koma Jamhuriyar Nijar”: Buhari ya magantu kan zaryar da wasu ke yi a gidansa na Daura

Buhari
Muhammadu Buhari ya dawo daga masallaci Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muhammadu Buhari ya yi nasara a shekaru 8?

"Ubangiji ya ba ni dama in bautawa kasa ta, kuma na yi bakin kokari na. Ko abin da na yi ya isa, na bar mutane su zama alkalai."

- Muhammadu Buhari

Da aka tambaye shi ko kwalliya ta biya kudin sabulu ganin ya yi takara har sau hudu, Buhari ya nuna lamarin ba yadda dai aka so ba.

An rahoto shi ya na cewa an samu saukin ta’addancin Boko Haram lokacin da ya sauka, a halin yanzu ya na mahaifarsa a Daura.

Buhari ya ce mulkin Najeriya akwai wahala

Tsohon shugaban ya koka da cewa ‘yan Najeriya su na da wahalar jagoranta saboda su na ganin sun fi mai mulki sanin abin da ya dace.

Duk da yadda ta kasance a mulkinsa, Buhari ya ce idan ya ba mutum mukami, ya na kyale shi ya yi aikinsa, ya ce wannan ne rauninsa.

Kara karanta wannan

Ni na taimaki Buhari ya samu mulki, yana shiga Aso Rock ya juya mani baya - Ardo

A hirar da aka yi da shi a NTA, Mai girma Buhari ya nuna babu mamaki an samu wasu miyagu da su ka juya madafan iko a lokacinsa.

Buhari yake cewa ya amince a canza kudi daf da zai bar mulki ne saboda ya kare mutuncinsa kuma ya nuna arziki sai an yi gumi.

Ko a yau zai samu wata damar, Muhammadu Buhari yake cewa yadda ya yi mulki tsakanin 2015 da 2023, hakan dai zai sake maimaitawa.

Shugaba Buhari ya so ya tsere zuwa Nijar

An ji labari bayan kusan watanni shida da fita daga fadar Aso Rock, Muhammadu Buhari ya zanta da 'yan jarida, wannan ne karon farko.

Buhari ya nuna saura kiris ya tafi kasar Nijar saboda mutane sun dame shi, abin da ya hana shi ne rufe iyaka da gwamnatin Bola Tinubu ta yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel